Yan sandan Najeriya Sun Ceto Mutane 10 Da Aka Sace A Kano.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ceto fasinjoji 10 da ake zargin ‘yan bindiga sun sace bayan sun kai hari kan motar safa a kan hanyar Jos zuwa Kano a yankin karamar hukumar Doguwa, yayin da ake ci gaba da neman sauran mutane uku da aka sace.
Lamarin ya faru ne a yankin dajin Falgore, tsakanin ‘Gate Two’ na hanyar ‘Safer Highway’ da Dogo Dutse, inda wasu ‘yan bindiga suka tare wata motar Toyota Hiace mai lamba BKK 6824 XA, wadda ya fito tafiya daga Jos zuwa Kano.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Abdullahi Kiyawa, ya fitar, an bayyana cewa maharan—wadanda suka kunshi maza biyar dauke da adduna da bindiga—sun tare hanyar tare da sace fasinjoji 13 daga cikin mutane 20 da ke cikin motar.
KARANTA KUMA: Kano: ‘Yan Sanda Sun Dakile Shirin Amfani da Bam da Safarar Miyagun Kwayoyi
An ceto fasinjoji tara a yayin aikin ceto, yayin da wani mutum daya ya samu nasarar tserewa daga hannun masu garkuwar daga baya, lamarin da ya sa jimillar wadanda aka ceto suka kai 10.
A cewar ‘yan sandan, an kai fasinjojin da aka ceto zuwa Asibitin Koyarwa na Doguwa (Doguwa General Hospital) domin ba su kulawar likita.
Rundunar ta bayyana cewa wadanda aka ceton suna cikin koshin lafiya. Sai dai, mutane uku—namiji daya da mata biyu—har yanzu suna hannun masu garkuwar.
‘Yan sandan sun kara da cewa an tura karin tawagar jami’an tsaro na musamman, tare da tallafin ayyukan da suka dogara da bayanan sirri, domin gano maharan da suka tsere, ceto sauran mutanen da ke hannunsu, da kuma gurfanar da wadanda ke da hannu a lamarin gaban kotu.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Ibrahim Bakori, ya yaba wa mazauna yankin da direbobin motoci wadanda bayanan da suka bayar a kan kari suka ba da damar daukar matakin gaggawa, inda ya bayyana hadin gwiwar al’umma a matsayin muhimmin abu wajen samun nasarar aikin.
Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa rundunar ta kuduri aniyar kare rayuka da dukiyoyi a fadin jihar Kano, tare da yin kira ga mazauna yankin da su ci gaba da sanar da ‘yan sanda game da duk wani motsi na shakku ko ayyukan laifi ta hanyar zuwa tashar ‘yan sanda mafi kusa ko kuma ta lambobin wayar gaggawa na rundunar.
Aisha.Yahaya, Lagos



