Najeriya Ta Tura Tawaga Zuwa Taron Musulunci Na Duniya Na Ahmadiyya.

Kungiyar Ahmadiyya Muslim Jamaat ta Najeriya ta tura tawagar mambobi sama da 50 domin halartar taron Jalsa Salana na Burtaniya na shekarar 2026—daya daga cikin manyan tarukan Musulunci na shekara-shekara a duniya—wanda aka tsara gudanarwa daga ranar 24 zuwa 26 ga watan Yuli a Oakland Farm, Hadeeqatul Mahdi, Surrey, a kasar Burtaniya.
Wanda ke jagorantar tawagar Najeriyar shi ne Amir (Shugaban kasa) na kungiyar Ahmadiyya Muslim Jamaat ta Najeriya, Barrister Alatoye Folorunso Azeez, wanda zai shiga tare da dubban mahalarta daga sassan duniya daban-daban a wannan taro mai daukar kwana uku.
Ana sa ran taron, wanda shi ne karo na 60, zai ja hankalin mahalarta sama da 50,000 daga kasashe fiye da 90, tare da samar da dandamali na inganta zaman lafiya, fahimtar juna tsakanin addinai, tattaunawa tsakanin mabiya addinai daban-daban, da kuma hadin kan duniya baki daya.
Taron zai kunshi jawabai daga ‘yan majalisar dokoki, jami’an diflomasiyya, shugabannin addini, da sauran fitattun mutane, wadanda za su bayyana muhimmancin girmama juna, zaman lafiya tare, da hadin gwiwar kasa da kasa.
Babban abin da zai dauki hankali a taron shi ne jawabai na musamman daga Shugaban kungiyar Ahmadiyya ta duniya, Hazrat Mirza Masroor Ahmad (aba), wato Khalifatul Masih na Biyar. A yayin taron na kwana uku, ana sa ran zai gabatar da sakonni da suka shafi imani, zaman lafiya, adalci, da kuma rawar da addini ke takawa wajen tunkarar kalubalen duniya na zamani.
Za a watsa taron kai tsaye a duniya ta tashar Muslim Television Ahmadiyya (MTA) International, tare da watsa shirye-shiryen ta wasu tashoshin talabijin na kasa da kasa da na cikin gida sama da 20.
A Najeriya, tashoshin WAP TV, MiTV, da Tambarin TV Hausa za su sake watsa taron ga masu kallo a fadin kasar.
Kungiyoyin yada labarai da dama, ciki har da Nigerian Television Authority (NTA), Voice of Nigeria (VON), TVC Communications, Radio France Internationale (RFI) Hausa Service, MiTV, da Ben TV London, za su rika bayar da rahotanni da labarai game da taron.
Dr. Qasim Akinreti ne ke jagorantar tawagar ‘yan jarida ta Najeriya, kuma shi ne shugaban bangaren yada labarai na kungiyar Ahmadiyya Muslim Jamaat ta Najeriya. Har ila yau, taron zai ƙunshi watsa shirye-shirye kai-tsaye daga babban masallacin ƙasa na Ahmadiyya Muslim Jamaat da ke Ojokoro, Legas, da kuma cibiyar al’ummarsu da ke Idogo a Jihar Ogun, inda za a haɗa masu ibada da masu kallo da sauraro da sauran cibiyoyin Ahmadiyya a sassan duniya daban-daban.
A cewar wata sanarwa daga kungiyar Ahmadiyya Muslim Jamaat ta Najeriya, an shirya wannan taro ne domin karfafa rayuwar ruhaniya ta mahalarta, zurfafa fahimtarsu game da koyarwar Musulunci, da kuma karfafa mu’amala ta zaman lafiya tsakanin mutane masu bambancin addini da al’adu.
Mahalarta da sauran jama’a za su iya bibiyar shirye-shiryen taron ta hanyar manhajar wayar hannu ta ‘Jalsa Salana UK’ (wacce ake samu a shafukan Apple App Store da Google Play Store), da kuma ta shafukan YouTube, Facebook, Instagram, TikTok da sauran dandamalin yanar gizo.
Wannan taro na shekara-shekara yana daya daga cikin manyan tarukan kasa da kasa na kungiyar Ahmadiyya, inda ake hada masu bauta daga kasashe daban-daban domin inganta zaman lafiya, tausayi, da kuma hidima ga bil’adama.
Aisha.Yahaya, Lagos



