Ebola: Hukumar Africa CDC Na Neman A Kawo Karshen Haramcin Tafiye-Tafiye Zuwa Uganda.

Cibiyar Kula Da Cututtuka Ta Afirka da Africa CDC, ta nemi Amurka da ta dage takunkumin tafiye-tafiye da ta sanya wa Uganda, tana mai jayayya cewa kasar ta shawo kan barkewar cutar Ebola.
Da yake jawabi a taron kolin lafiya na Tarayyar Afirka a Ghana, Darakta Janar na CDC na Afirka Jean Kaseya ya ce Uganda ta shafe makonni uku ba tare da wani sabon lamari na Ebola ba kuma ta sallami majinyacinta na karshe a farkon wannan watan. Ya yi gargadin cewa bai kamata a hukunta kasashe ba saboda bayyana gaskiya game da barkewar cutar.
Amurka ta kara tsaurara takunkumin tafiye-tafiye kan Uganda, Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, da Sudan ta Kudu yayin da barkewar cutar ta bazu a yankin.
KARANTA KUMA: Barkewar Ebola a Congo Zai Iya Zama Mafi Muni – Afirka CDC
Yayin da take adawa da haramcin tafiye-tafiye, Kaseya ya yi gargadin cewa barkewar cutar a DRC na kara tabarbarewa da sauri, inda aka tabbatar da kamuwa da cutar sama da 2,300 da kuma mutuwar sama da 900 tun daga watan Mayu.
Africa CDC ta ce ana bukatar kusan dala biliyan 1.4 don dakile barkewar cutar, tana gargadin cewa ba tare da gaggawar tallafin kudi na kasa da kasa da kuma karfafa sa ido kan cututtuka ba, rikicin zai iya zama mafi muni da ba a taba gani a tarihi.
Labaran Afrika/Aisha.Yahaya, Lagos



