Afirka

UNHCR Ta Bayar Da Rahoton Mutuwar Da Bacewar Bakin Haure Guda 144

Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) ta bayyana cewa an samu rahoton mutuwar ko bacewar akalla bakin haure 144 a gabar tekun kasar Mauritania, bayan sun yi yunkurin ketare teku zuwa Turai ta hanyar da ke cike da hadari.

UNHCR ta bayyana hakan ne a ranar Talata da ya gabata bayan gudanar da ayyukan ceto guda uku a Mauritania tsakanin ranakun 14 da 18 ga watan Yuli, inda ya yi kira ga gwamnatoci da su fadada damar samun ilimi da ayyukan yi domin rage haduran da ke haifar da hijira ta hanyoyin da ba su dace ba.

A cewar hukumar, mutane 143 ne suka mutu a cikin jirgin ruwa guda daya da ya tashi daga Bufaloto a kasar Gambia, wanda aka ceto a ranar 18 ga watan Yuli bayan ya yi ta yawo a teku na tsawon kwanaki 25.

Jirgin ya iso tare da gawarwakin wadanda suka mutu da kuma mutane 38 da suka tsira, wadanda suka samu tallafin jin kai daga jami’an UNHCR a wurin sauka da ke Nouadhibou, Mauritania.

Kakakin UNHCR, Matt Saltmarsh, ya shaida wa taron manema labarai a Geneva cewa yara biyu sun tsira daga tafiyar amma sun rasa dukkan ‘yan uwansu a yayin tafiyar. Ya ce a yanzu yaran suna samun kulawar likita a asibiti.

Saltmarsh ya ce hukumar ba za ta iya tabbatarwa nan take ba ko wadanda suka mutu sun rasu ne sakamakon nutsewa, yunwa, kishirwa ko wasu dalilai. Ya kara da cewa wadanda suka mutu ‘yan kasashe daban-daban ne na yankin kudu da hamadar Sahara.

Hukumar ta kuma bayar da rahoton cewa an samu gawar mutum daya a cikin wani jirgin ruwan daban da ya isa Mauritania a ranar 14 ga watan Yuli.

A dunkule, ayyukan ceto guda uku da aka gudanar tsakanin ranakun 14 da 18 ga watan Yuli sun ceci rayukan mutane 387, a cewar UNHCR.

Hukumar ta bayyana cewa an samu saukewar 17 da aka sauke bakin haure a Nouakchott ya zuwa yanzu a shekarar 2026, inda aka ceto mutane 2,147 baki daya.

Duk da raguwar adadin mutanen da ke isa Turai ta ruwa, hukumar UNHCR ta yi gargadin cewa yawan mace-mace a hanyoyin da bakin haure ke bi yana ci gaba da kasancewa a matakin da ke haifar da damuwa sosai.

Bisa alkaluman Majalisar Dinkin Duniya, sama da bakin haure da ‘yan gudun hijira 40,000 ne suka isa Turai ta ruwa a shekarar 2026, idan aka kwatanta da mutane 65,407 a irin wannan lokacin na shekarar 2025. Sai dai, hukumar ta ce mace-mace da bacewar mutane a wadannan hanyoyi na ci gaba da faruwa a matakin da ba za a iya amincewa da shi ba.

 

 

Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button