DuniyaKiwon Lafiya

Wata Mata ‘Yar Kasar Australia Ya Haifi ‘Yan Hudu Masu Kama Da Juna.

Wata mata ‘yar kasar Australia ta haifi ‘yan hudu mata masu kama da juna ta hanyar daukar ciki na dabi’a—wani abu da ba kasafai ake samunsa ba—bayan da likitoci suka bayyana cikin nata a matsayin mai “hadari matuka,” kamar yadda Asibitin Royal Brisbane and Women’s Hospital ya bayyana.

An haifi ‘yan matan hudun ne ta hanyar tiyata a ranar 14 ga watan Yuli, bayan sun shafe makonni 28 da kwana hudu a cikin mahaifa. Su ‘yan hudu ne da suka fito daga kwai guda daya da ya rarrabu zuwa jarirai hudu (monozygotic quadruplets).

Mahaifiyarsu, Jenitar Na’amoana mai shekaru 34, da mijinta Jortham, tuni suna da wasu yara hudu, kuma an ce sun yi matukar mamaki lokacin da suka gano cewa za su haifi ‘yan hudu.

Dr. Alexa Bendall, kwararriyar likita a fannin kula da lafiyar mata masu ciki da jarirai (maternal-foetal medicine specialist), wadda ta kula da cikin, ta ce haihuwar ‘yan hudu masu kama da juna na faruwa ne “sau daya a cikin ciki miliyan 15,” sannan ta kara da cewa, “amma batun raba mahaifa guda daya—wannan abu ne da ba a taba jin irinsa ba.”

Ta bayyana cewa cikin yana da hadari sosai, lamarin da ya sa likitoci suka kwantar da Na’amoana a asibiti tun tana da cikin makonni 25 domin sa ido sosai kan yanayinta.

“A kodayaushe muna cewa idan muka iya kai ta matakin makonni 28, to za mu yi nasara,” in ji Bendall.

“Don haka, samun jarirai hudu masu kyau da lafiya da aka haifa bayan makonni 28 da kwana hudu abu ne mai ban mamaki, kuma muna matukar farin cikin kasancewa cikin wannan lamari,” ta kara da cewa.

Jenitar ta dauki dukkan lamarin cikin nutsuwa tun daga farko… ta samu nasarar kaucewa duk wata matsala ko hadari, ita da jariranta,” in ji Bendall.

An sanya wa jariran sunayen Emily, Harriet, Catherine, da Alexa; inda aka sanya wa jaririya ta hudu sunan Dr. Bendall, wadda ta bayyana hakan a matsayin “girmamawa mai kyau.”

Har yanzu jariran suna sashin kula da jarirai masu bukatar kulawa ta musamman (neonatal intensive care unit), inda ake sa ran za su ci gaba da zama har sai sun kai lokacin da ya kamata a haife su (cikakken lokacin ciki). A cewar Bendall, “a halin yanzu suna cikin koshin lafiya sosai.”

Sauran ‘ya’yan ma’auratan suna da shekaru tsakanin daya zuwa 10. Domin shirye-shiryen karuwar iyalin, kwanan nan Na’amoana ta fara yakin neman tallafin kudi ta yanar gizo domin sayen mota mai daukar mutane akalla 10.

KARANTA KUMA: NHIA na bikin haihuwar jarirai hudu na farko a karkashin tsarin CEmONC

A cikin sakon da ta wallafa tare da yakin neman tallafin, wanda ya tara sama da Dalar Australiya 37,000 (fam 19,261), ta rubuta cewa:

“Jariranmu hudu masu daraja sun iso duniya lafiya, kuma yayin da zukatanmu ke cike da godiya, hakikanin nauyin kula da jarirai hudu a lokaci guda ya haifar da kalubalen da ba mu taba tunanin za su iya faruwa ba.”

Haihuwar jarirai hudu ta dabi’a (ba tare da amfani da hanyoyin taimakon haihuwa na likitanci ba) abu ne mai matukar wuyar gaske; likitoci na kiyasta cewa hakan na faruwa ne sau daya a cikin haihuwa 700,000.

 

 

BBC/Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button