Senegal Ta Amince Da Neman Sakatare-Janar Na Majalisar Dinkin Duniya Macky Sall

Gwamnatin Senegal ta amince a hukumance da takarar tsohon Shugaban kasa Macky Sall na neman mukamin Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya mai zuwa, duk da sabanin siyasar da aka taba samu a baya tsakanin gwamnatinsa da gwamnatin da ke kan karagar mulki a yanzu.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Senegal ce ta sanar da wannan amincewa bayan umarnin da Shugaba Bassirou Diomaye Faye ya bayar ga ofisoshin jakadancin kasar da ke sassan duniya, na su nemi goyon baya ga takarar Sall.
Wannan mataki ya zo ne kwanaki kadan bayan Sall ya kai ziyararsa ta farko a birnin Dakar tun bayan barin mukaminsa a shekarar 2024, inda ya gana da Shugaba Faye.
KARANTA KUMA: Senegal ta musanta goyon bayan Sall na neman mukamin Sakatare-Janar na MDD
Wannan mataki na amincewa ya nuna babban sauyi a manufofin gwamnati, kasancewar a baya gwamnatin Faye ta ki goyon bayan Sall, inda ta zarge shi da danniya ta fuskar siyasa da kuma boye muhimman bayanai game da tattalin arziki a shekarun karshe na mulkinsa.
A cewar Ma’aikatar Harkokin Waje, Shugaba Faye na ganin cewa takarar Sall tana da amfani ga Senegal da kuma nahiyar Afirka baki daya.
Tun da farko a wannan shekara, kasar Burundi—wacce ke rike da shugabancin kungiyar Tarayyar Afirka a yanzu—ita ce ta fara gabatar da sunan Sall domin neman wannan babban mukami na Majalisar Dinkin Duniya.
Sai dai, dawowar tasa zuwa Senegal ta sake tayar da kiran masu suka da ke neman a yi bincike da kuma daukar mataki kan rikice-rikicen da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane a shekarun karshe na mulkinsa.
Aisha.Yahaya, Lagos



