Hukumomin Uganda Za Sun Sallami Majiyyacin Ebola Na Karshe.

Wani mai magana da yawun gwamnatin Uganda ya bayyana cewa, za a sallami majiyyacin Ebola na ƙarshe a ƙasar ranar Alhamis da ta gabata matakin da zai fara ƙidayar kwanaki 42 da ka iya kai ga ayyana ƙasar a matsayin wadda ta kubuta daga cutar.
Bisa bayanan gwamnati, wannan annoba mai yaɗuwa—wadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana a matsayin gaggawar lafiyar jama’a a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo (DRC) a watan Mayu—ta haifar da mutane 2,011 da aka tabbatar sun kamu da cutar da kuma mutuwar mutane 754 a DRC zuwa ranar Laraba Da ta gabata.
Wani shafin yanar gizo na ma’aikatar lafiya ta Uganda ya nuna cewa, zuwa ranar Alhamis, mutane 17 ne suka warke, yayin da ake ci gaba da kula da mutum ɗaya a cibiyar killace masu cutar, kuma an samu mutuwar mutane biyu. Rahoton ya nuna cewa mutane biyar sun kamu da cutar a cikin ƙasar, yayin da 15 suka shigo da ita daga waje.
KARANTA KUMA: Abokan Hulɗa a Fannin Agaji Sun Nemi Kuɗaɗe don Yaki da Ebola a Uganda
Dukkan waɗannan lokuta na kamuwa da cutar suna da alaƙa da nau’in ƙwayar cuta mai wuyar gani ta *Bundibugyo*, kuma WHO ta bayyana cewa ita ce annoba ta uku mafi muni da aka taɓa rubutawa a tarihi.
Alan Kasujja, mai magana da yawun gwamnatin Uganda, ya bayyana a wani saƙo da ya wallafa a shafin X a ƙarshen ranar Laraba da ta gabata cewa, za a sallami wani majiyyaci daga cibiyar killace masu cutar a Asibitin Mulago National Referral Hospital, wanda ke babban birnin ƙasar, a ranar Alhamis Da ta gabata.
Kasujja ya ce sallamar majiyyacin za ta fara ƙidayar lokacin jira da Hukumar Lafiya ta Duniya ta kayyade kafin a iya ayyana cewa annobar ta ƙare. “Idan hakan ya faru, Uganda za ta fara ƙidayar kwanakin,” in ji Kasujja.
“Idan kwanaki 42 suka shude ba tare da an samu sabon mai ɗauke da cutar ba, ƙa’idojin WHO sun tanadi cewa za a ayyana mu a matsayin waɗanda suka kubuta daga Ebola.”
Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos



