
Gwamnatin jihar Nasarawa, arewa maso tsakiyar Najeriya, ta yi alƙawarin neman haɗin gwiwa da hedikwatar Bankin Duniya ta Najeriya don binciko dabarun magance ƙalubalen zaizayar ƙasa a jihar.
Kwamishinar Muhalli da Albarkatun Ƙasa, Dr. Margaret Elayo, ta bayyana haka ne a lokacin rangadin duba da aikin kula da zaizayar ƙasa da ruwa na Najeriya tare da Bankin Zuba Jari na Turai, kwamitin NEWMAP-EIB a garin Tudun Kasira na ƙaramar hukumar Lafia ta jihar.
Ta yi alƙawarin ɗaukar mataki nan take ta hanyar haɗin gwiwa da hedikwatar bankin duniya ta Najeriya don ba da kuɗi da kuma aiwatar da aikin ceto.

A lokacin duba, ɗalibai da mazauna Tudun Kasira sun yi kira ga gwamnatin Jihar Nasarawa da ta gyara wani babban wurin zaizayar ƙasa wanda ke barazana ga rayuwarsu da makomar karatunsu.
KARANTA KUMA: Najeriya Ta Yi Bitar Tsarin Manufofin Zaizayar Ƙasa da Kula da Ambaliyar Ruwa
Wata ɗaliba, Esther Jatau, wacce ke fuskantar mummunan hanyar da kowace safiya ta isa makarantarta, ta fashe da kuka yayin da take magana da Kwamishinan.
“Mama, don Allah, muna buƙatar taimakon gwamnatin jihar,” in ji Esther. “Wannan zaizayar ƙasa babbar barazana ce ga iliminmu. Da yawa daga cikinmu ba mu da wata hanya ta daban. Burina shine in zama likita ko injiniya, amma na fara jin tsoron zuwa makaranta saboda wannan zaizayar ƙasa.”

Babban ramin ya sa dalibai ba su da wata hanyar daban, lamarin da ya tilasta musu ratsawa ta wurare masu matukar hadari domin isa ajijinwasu
Aisha. Yahaya, Lagos



