Qatar Ta Ce Kokarin Shiga Tsakanin Amurka Da Iran Na Ci Gaba

Firayim Ministan Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al-Thani ya bayyana cewa kokarin shiga tsakani tsakanin Amurka da Iran na ci gaba domin hana kara ta’azzara yanayi a yankin.
A cewar rahotanni Al-Thani ya ce Washington har yanzu tana da muradin cimma yarjejeniya duk da sakamakon zaben tsakiyar wa’adi da aka gudanar a ranar Talata.
Ya ce Amurka ba ta canza matsayinta na neman mafita ta hanyar diflomasiyya ba kuma an samu gagarumin ci gaba a tattaunawar da ake yi.
Al-Thani ya nuna kwarin gwiwar cewa za a iya cimma matsaya inda ya ce “Ba za mu iya jira har sai mun samu cikakkiyar yarjejeniya ba muna fatan cimma yarjejeniya mai kyau.”
KARANTA KUMA: Masu Shiga Tsakani Daga Qatar Za Su Gudanar Da Tattaunawa Daban-daban Da Amurka Da Iran
Sai dai Tehran ta gabatar da wani shiri na kwanaki bakwai domin warware takaddamar shirin da ta fara gabatarwa tun a watan Satumba.
Shirin ya bukaci Washington ta dage takunkumin da ta kakaba wa tashoshin jiragen ruwa na Iran ta saki kadarorin Iran da aka daskarar tare da amincewa da wata hanyar wucewa ta Mashigar Hormuz (Strait of Hormuz) wadda Iran ke goyon baya domin ba da damar sake bude wannan hanyar ruwa.



