Afirka

Majalisar kasar Habasha Ta Sake Zaben Abiy Ahmed A Matsayin Firaminista

Majalisar dokokin kasar Habasha ta sake zaben Abiy Ahmed a matsayin Firayim Minista na wa’adin shekaru biyar bayan babban zaben da aka gudanar a ranar 1 ga watan Yuni.

Ahmed ya karbi rantsuwar kama aiki a wani biki da Shugaba Taye Atske Selassie da sauran manyan jami’an gwamnati suka halarta inda ya fara sabon wa’adinsa a hukumance.

Jam’iyyarsa mai mulki ta Prosperity Party ta lashe kujeru 438 cikin kujeru 547 na majalisar dokoki a zaben, lamarin da ya ba shi damar sake samun nasarar zaben.

KARANTA KUMA: Sake Zabe: Najeriya ta taya Firayim Ministan Habasha murna

Wannan ci gaba ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da sabon rikici tsakanin sojojin gwamnatin Habasha da sabuwar kungiyar ‘Ethiopian Peoples’ Forces Alliance for Survival’ wacce ke neman hambarar da gwamnatin.

Gwamnatin Habasha ta zargi kasashen da ke makwabtaka da ita ciki har da Eritrea da goyon bayan kungiyoyi masu dauke da makamai da ke da hannu a rikicin.

Habasha ta sanar da rufe ofishin jakadancinta a Eritrea lamarin da ya kara dagula alaka tsakanin kasashen biyu makwabta.

Sake barkewar fada da kuma taku sakar diflomasiyya na haifar da sabbin kalubale ga Ahmed yayin da yake fara sabon wa’adinsa na shekaru biyar.

 

Africanews/Ladan Nasidi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button