Fitattun Labarai

Shugaba Tinubu Ya Yi Allah-wadai Da kKsan Da Aka Yi A Neja Ya kuma Bayar Da Umarnin Ceto Wadanda Aka Sace

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da sace tare da kashe fararen hula marasa laifi da wasu ‘yan ta’adda suka yi a Jihar Neja inda ya umurci Rundunar Soji da Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da sauran hukumomin tsaro da leken asiri su hada karfi da karfe domin ceto wadanda aka sace din.

Wannan umarni yana cikin wata sanarwa ce da mai bai wa Shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru Mista Bayo Onanuga ya sanya wa hannu a ranar Talata.

Yayin da yake jaddada cewa ba za a bar wadanda suka kai harin ba tare da an hukunta su ba Shugaban ya bayyana masu aikata laifin a matsayin makiyan zaman lafiya da ‘yan adam tare da nanata cewa za a gurfanar da su gaban kuliya domin fuskantar shari’a.

“Wadanda suka kai wannan hari na rashin jaruntaka kan ‘yan Najeriya marasa makami kuma makiyan zaman lafiya ne da makiyan ‘yan adam kuma ba za su tsira ba” in ji shi.

 

KARANTA KUMA: Sojoji Sun Dakile Kokarin ‘Yan Ta’adda na Sace Mutane a Zamfara

Ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda aka kashe tare da ba wa ‘yan uwan ​​wadanda aka sace tabbacin cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai an ceto ‘yan uwansu cikin aminci.

“Ba ku kadai ba ne. Daukacin al’ummar kasar nan suna tare da ku cikin wannan hali na bakin ciki. Ba za mu huta ba har sai an dawo muku da ‘ya’yanku maza da mata da iyayenku mata da maza, cikin aminci” in ji Shugaban.

Ya kuma umurci shugabannin hukumomin tsaro da su rika ba da bayanai akai-akai game da aikin ceto har sai an gano dukkan wadanda aka sace.

Yayin da yake sake jaddada kudirin gwamnati na kare rayuka da al’ummomi Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ayyukan ta’addanci ba za su tsoratar da kasar ba.

“Ta’addanci ba zai tsoratar da Najeriya ba. Za mu kare al’ummarmu mu kare yankunanmu tare da mutunta tsarkin rayuwar dan Adam” in ji shi.

Shugaban ya kuma bai wa gwamnatin Jihar Neja da al’ummomin da abin ya shafa tabbacin goyon bayan Gwamnatin Tarayya wajen ayyukan farfadowa da tallafi da kuma karfafa tsaro.

 

Ladan Nasidi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button