Najeriya

Gwamnan Borno Ya Nuna Godiyasa Ga Shugaba Tinubu Bisa Sake Tsayar Da Shettima Takara.

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya nuna godiyarsa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa sake zaban Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Gwamna Zulum ya bayyana wannan mataki a matsayin “abin alfahari ga Jihar Borno da kuma daukacin yankin Arewacin Najeriya.”

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis da ta gabata bayan ziyarar godiya da ya kai wa Shugaban Kasa a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, Gwamnan ya ce ya je fadar ne domin isar da sakon godiyar al’ummar Borno tare da neman amincewar Shugaban Kasa domin tawagar gwamnoni da wakilai daga yankin Arewa maso Gabas su kai masa ziyarar godiya ta musamman.

Ya ce Shugaba Tinubu ya amince da bukatar, inda ya jaddada cewa gwamnonin jihohi shida na yankin Arewa maso Gabas za su ziyarci Shugaban Kasar a mako mai zuwa.

Gwamna Zulum ya ce: “Tawagar za ta yi amfani da ziyarar wajen nuna godiya a madadin gwamnoni da al’ummar yankin Arewa maso Gabas bisa amincewar da aka nuna ga Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima.”

Yayin da yake nazarin muhimmancin wannan zabe, ya bayyana shi a matsayin wani babban ci gaba mai tarihi, inda ya lura cewa wannan shi ne karo na farko da aka sake zaban dan Jihar Borno domin ya ci gaba da rike mukamin Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya.

Gwamnan ya tuna cewa duk da cewa an kusa samun irin wannan dama a zamanin Jakada Babagana Kingibe, hakan bai tabbata ba.

 

 

Aisha.Yahaya, Lagos

 

 

Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button