
Gwamnan Jihar Oyo Seyi Makinde ya sake jaddada goyon bayan gwamnatinsa ga cibiyoyin addini da ke aiki don inganta zaman lafiya hadin kai da ci gaban jihar.
Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin bikin cika shekaru 120 da kafuwar Cocin First Baptist da ke Idikan Ibadan babban birnin jihar.
Gwamnan ya taya cocin da kungiyar Nigerian Baptist Convention murna kan wannan muhimmin lokaci inda ya bayyana cocin a matsayin cibiya mai dadadden tarihi da ta bayar da gudummawa wajen ci gaban ruhaniya da zamantakewa a jihar.
Ya ce” Ina taya Cocin First Baptist Idikan murna kan bikin cika shekaru 120. Addu’ata ita ce daukakar shekaru 120 masu zuwa ta zarce ta shekaru 120 da suka gabata.”
Ya yaba wa shugabannin cocin da mambobinta kan gudummawar da suka bayar wajen hidimar al’umma da gina kasa a tsawon shekaru 120 da suka gabata.
KARANTA KUMA: Gwamna Makinde ya ziyarci dalibai da malamai daga Oriire da aka ceto a asibiti
Shugaban kungiyar Nigerian Baptist Convention Rev. Dr David Idowu ya bai wa Gwamnan kyautar karramawa inda ya gode masa bisa halartar bikin da kuma bayar da gudummawar motar bas kirar Hummer domin tallafawa ayyukan wa’azin cocin.
Bikin ya kunshi addu’o’i na musamman domin Gwamna Makinde Jihar Oyo da kuma Najeriya.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai tsohon shugaban kungiyar Nigerian Baptist Convention kuma tsohon shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) Rev. Dr Samson Ayokunle Shugaban Ibadan Baptist Conference Rev. Dr Oyekola Bamidele Faston Cocin First Baptist Rev. Dr Solomon Oyelami da kuma Chief Niyi Akintola SAN.
Safina Umar Farouk.



