Afirka

Sojojin Nijar Sun Sake Karbe Ikon Sansanin Jiragen Sama

Sulaiman Ibrahim Muhammada

Nijar ta ce ta sake kwace sansanin sojin sama bayan da sojoji ‘yan Mutineers suka yi garkuwa da sojoji a wani sansanin soja da ke kusa da babban birnin Niamey ranar Asabar a matsayin sabon kalubale ga shugaban soja Abdourahamane Tiani yayin da gwamnatinsa ke fafutukar shawo kan rikicin jihadi.

Wannan harin ya nuna tashin hankali a cikin sojojin Nijar wadanda suka sha kashi a fagen daga akai-akai yayin da suke fafatawa da kungiyar al-Qaeda da reshenta na kungiyar IS ta Yammacin Afirka.

An yi ta jin karar fashewar bama-bamai da harbe-harbe a fadin Niamey da sanyin safiyar ranar Asabar ciki har da sansanin sojin sama na soja da kuma kusa da fadar shugaban kasa.

 

KARANTA KUMA: Sojojin Nijar Sun Yi Fada Da Masu Tada Kayar Baya Kusa da Filin Jirgin Sama na Babban Birnin

Cikin sansanin yana cikin ginin da filin jirgin saman farar hula na Niamey yake sansanin sojojin sama yana dauke da jiragen sama marasa matuki da kuma wani rukunin yaki da ta’addanci na kungiyar kasashen Sahel AES wanda ya hada da Nijar Mali da Burkina Faso.

Sojojin Rasha da Italiya suma suna nan a wurin.

Rundunar sojojin Afirka wacce Kiremlin ke iko da ita ta sami buƙatar taimako wajen kawar da masu bore a Niamey cewar Viktor Voropaev jakadan Rasha a Nijar a ranar Asabar a wata hira da kamfanin dillancin labarai na TASS.

Kafin harin ranar Asabar an riga an kai hari kan sansanin sojin sama sau biyu a wannan shekarar a watan Janairu daga ƙungiyar IS kuma a watan Yuni daga ƙungiyar al Qaeda ta yankin.

Kafafen yada labarai na kasar Niger sun ce a daren Asabar cewa harin ya shafi “ɗaruruwan sojoji da ba su ji ba ba su gani ba” kuma yaƙin ya ɗauki tsawon sa’o’i da dama yayin da dakarun da ke biyayya ga shugaban soja Tiani ke ƙoƙarin sake kwace iko.

Majiyoyin tsaro uku sun ce rundunar tsaron shugaban ƙasa ta yi gangami don kare Tiani. Tiani bai bayyana a bainar jama’a ba har zuwa safiyar Lahadi.

Jami’an soji ne ke mulkin Nijar ƙasar Afirka ta Yamma mai arzikin uranium mai da albarkatun zinare tun bayan juyin mulkin da aka yi a watan Yulin 2023 wanda ya hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum.

 

 

Reuters/Sulaiman Ibrahim Muhammada.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button