
Wani girgizar kasa mai karfin maki 7.7 ta afku a kudancin kasar Panama inda ta lalata gine-gine tare da sa dubban mutane fitowa kan tituna duk da cewa kasar ta tsira daga mummunar barna ko asarar rayuka.
Hukumar Kula da Yanayin Kasa ta Amurka (USGS) ta bayyana cewa girgizar kasar ta faru ne a zurfin kilomita 12.6 kuma cibiyarta ta kasance a wani yanki da ba a cika samun yawan jama’a ba kimanin kilomita 200 daga babban birnin kasar Panama City. Hukumar ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar samun wadanda suka jikkata.
An bayar da rahoton cewa harkoki na tafiya yadda ya kamata a Tashar Ruwa ta Panama (Panama Canal) da kuma ma’adinan jan karfe na Cobre Panama yayin da Filin Jirgin Sama na Duniya na Tocumen ya janye dokar dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na wucin gadi.
Shugaba Raul Mulino ya ziyarci birnin Penonome wanda ke tsakiyar nisan da ke tsakanin cibiyar girgizar kasar da kuma Panama City a wurin ne aka samu rushewar wasu gine-gine da kuma lalacewar wani coci.
KARANTA KUMA: Panama Na Neman Alluran Rigakafin COVID-19 Na Rasha Guda Miliyan 3
USGS ta yi hasashen cewa kimanin mutane 43,000 a Panama ne ke zaune a yankunan da girgizar kasar ta shafa sosai.
Nestor Luque darektan cibiyar nazarin ilimin kasa ta Panama ya danganta girgizar kasar da tsarin layin tsagewar kasa na Azuero-Sona (Azuero-Sona Fault System) inda ya bayyana cewa yana tara matsin lamba mai yawa wanda ke sakin kansa lokaci-lokaci.
“Alamun girgizar kasar sun bazu ko’ina a fadin kasar shi ya sa aka ji tasirinta a ko’ina” cewar Luque.
Wani ma’aikacin kula da gine-gine Victor Pinzon ya ba da labarin yadda ya ga masu wanke tagogin manyan gine-gine suna fuskantar girgizar.
“Abin mamaki ne yadda ba su mutu ba sun yi kama da mutanen da ke ta juyawa a cikin gadon zane (hammock)” in ji shi.
Shugaban hukumar kare fararen hula ta Panama Omar Smith ya bayyana cewa an samu rahoton tasirin girgizar kasar a Chitre babban birnin lardin Herrera da kuma yankunan gabar teku na lardin Los Santos.
Hukumar USGS ta yi hasashen cewa asarar tattalin arziki na iya kaiwa tsakanin kashi 1 zuwa 10 na jimillar kayayyaki da ayyukan da kasar Panama ke samarwa (GDP) yayin da kamfanin samar da wutar lantarki na Naturgy ya bayar da rahoton katsewar wuta a larduna shida.
An shirya gudanar da atisayen kwashe jama’a daga wuraren hadari a fadin kasar Panama a ranar Litinin mai zuwa domin gwada karfin kasar wajen tunkarar yanayin gaggawa.



