‘Yan Tawagar Falconets Sun Taru A Abuja Domin Shirye-Shiryen Gasar Cin Kofin Duniya Na ‘Yan Kasa Da Shekaru 20.

Kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya ‘yan kasa da shekaru 20, wato Falconets, ta fara shirye-shiryen tunkarar gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA U-20 ta shekarar 2026, wadda za a gudanar a kasar Poland daga ranar 5 zuwa 27 ga watan Satumba.
An gayyaci ‘yan wasa 28 baki daya, inda 16 daga cikinsu suka riga suka isa sansanin horarwa yayin da ake ci gaba da gudanar da shirye-shiryen wannan gasa ta duniya. Ana sa ran karin ‘yan wasan da aka gayyata za su shiga tawagar a kwanaki masu zuwa.
Kungiyar masu horarwa, karkashin jagorancin Koci Moses Aduku, ta fara aiki nan take tare da gudanar da atisaye mai tsanani domin inganta tawagar, yayin da ake fatan ganin sun sake yin rawar gani a matakin duniya.
Falconets sun samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya ne bayan sun nuna bajinta a matakin neman cancanta, inda suka doke Rwanda da jimillar kwallaye 5-0 a zagaye na biyu, sannan suka doke Senegal da ci 3-2 a jimilla a zagayen da ya gabaci na karshe.
Sun tabbatar da zuwansu Poland bayan sun doke Malawi da ci 3-2 a jimilla a zagayen karshe na neman cancanta, lamarin da ya kara karfafa tarihin Najeriya a matsayin kasa daya tilo a Afirka da ta taba samun tikitin shiga dukkan gasannin cin kofin duniya na mata na FIFA U-20 tun lokacin da aka fara gasar a shekarar 2002.
KARANTA KARIN BAYANI: Poland 2026: An sanya Falconets a rukunin Spain, China, da New Caledonia
Najeriya na daya daga cikin kungiyoyin da suka fi samun nasara a tarihin gasar, inda ta zo ta biyu a shekarun 2010 da 2014, tare da kai matakin kusa da na karshe a shekarar 2012.
A gasar da ta gabata da aka gudanar a Colombia a shekarar 2024, Falconets sun fara gasar ne da nasarar ci 1-0 a kan Korea ta Kudu kafin su tsallake zuwa zagayen kungiyoyi 16, inda Japan ta fitar da su daga gasar.
Bayan an sanya su a Rukunin F tare da Spain, China, da Paraguay, Falconets za su yi kokarin dogaro da tarihin nasarorin da suka gabata domin fafutukar lashe kofin duniya na mata na FIFA U-20 a karon farko a tarihi.
Aisha.Yahaya, Lagos



