IMF Za Ta Ci Gaba Da Tattaunawa Kan Shirin Tallafawa Uganda A Watan Satumba

Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya bayyana cewa zai tura tawagar ma’aikatansa zuwa Uganda a watan Satumba domin ci gaba da tattaunawa kan sabon shirin tallafawa wannan kasa ta Gabashin Afirka.
Wakilin IMF a Uganda Sébastien Walker ne ya bayyana hakan yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan sabon shirin biyo bayan karewar wa’adin tsohon shirin tallafin da IMF ta bai wa Uganda a shekarar 2024.
Daga baya Uganda ta nemi a samar da sabon shirin amma bangarorin biyu ba su cimma matsaya ba tukuna.
Walker ya ce tattaunawar ta kasance mai amfani duk da cewa ana bukatar karin ci gaba kafin a iya cimma matsaya ta karshe.
A cewarsHI ana sa ran tawagar da aka shirya tura wa a watan Satumba za ta taimaka wajen ciyar da tattaunawar gaba da kuma tafiyar da tsarin zuwa ga sabuwar yarjejeniyar tallafi.
Tattalin arzikin Uganda ya ci gaba da samun ci gaba mai karfi kuma ana sa ran zai samu karin karfi sakamakon fara hako danyen mai da ake shirin yi nan ba da jimawa ba.
Sai dai, Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya bayyana cewa kasar na ci gaba da fuskantar nauyin biyan basussuka mai yawa da kuma raunin yanayin harkokin kudi na gwamnati; wadannan abubuwa ne masu matukar muhimmanci da ake la’akari da su a cikin tattaunawar da ake gudanarwa.
Reuters/LADAN NASIDI.



