Majalisar Dattawan Najeriya Ta Amince Da Kudirin Soke Dokar NAICOM Da Kuma Sake Kafa Ta.

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kudirin dokar soke Dokar Hukumar Kula da Inshora ta Kasa (NAICOM) ta shekarar 1997, tare da sake kafa Dokar na Hukumar Kula da Tsarin Inshora ta Kasa ta shekarar 2026.
Wannan matakin ya biyo bayan gabatar da rahoton Kwamitin Harkokin Banki, Inshora da sauran Batutuwan Kudi a zauren majalisar a ranar Talata da ta gabata.
Shugaban kwamitin, Sanata Adetokunbo Abiru, ya yin da gabatar da rahoton, ya bayyana cewa kudirin na da nufin soke tsohuwar dokar hukumar inshora tare da kafa sabuwar dokar hukumar kula da tsarin inshora.
KARANTA KUMA: Majalisar Dattawan Najeriya ta fadada bincike kan shirin kare makarantu
Sanata Abiru ya bayyana cewa tsohuwar dokar ta tsufa, ba ta dace da yanayin yau ko kuma ka’idojin aiki na duniya ba, sannan ta gaza tafiya da sauye-sauyen da ke faruwa a fannin inshora.
Ya ce hakan ya bayyana gibba da dama a cikin dokar, lamarin da ya sa ake bukatar yin gyare-gyare cikin gaggawa.
A cewarsa, Dokar Inshora ta Kasa ta shekarar 1997 ba ta biyan bukatun ci gaban tattalin arziki da na fannin kasuwancin inshora yadda ya kamata.
Sanata Abiru ya ce kudirin na da nufin tabbatar da ‘yancin hukumar da kuma karfafa ikonta na gudanar da ayyuka da yanke hukunci ba tare da tsoma bakin da bai dace ba. Haka kuma, ya ce kudirin zai bai wa hukumar karin iko wajen musayar bayanai da yin hadin gwiwa da hukumomin da ke kula da tsari da sa ido a cikin gida da kuma kasashen waje.
Ya kara da cewa, kudirin ya jaddada bukatar hukumar ta kunshi mutanen da ke da kwarewa ta musamman a fannonin inshora, sarrafa hadari, harkokin kudi, shari’a, da kuma tsarin gudanar da kamfanoni.
Ya ce kudirin ya kuma gabatar da matakan hukunci da tilasta bin doka, kamar kara yawan kudaden tara da dakatar da lasisin aiki, da sauransu.
Ya bayyana cewa kudirin ya kuma tanadi hana mutane rike mukamai a kamfanonin inshora idan aka same su da hannu wajen gazawa ko matsaloli.
Ya yi nuni da cewa babban manufar hukumar ita ce tabbatar da ingantaccen gudanarwa, sa-ido, tsara dokoki, kulawa, gaskiya, da kuma ci gaban harkokin inshora a Najeriya.
Ya bayyana cewa kudirin na neman samar da kariya ga hukumar da ma’aikatanta daga tuhume-tuhume ko kararrakin da ka iya tasowa yayin gudanar da ayyukansu da ikonsu.
A cewarsa, kudirin ya ba da shawarar sauya sunan hukumar daga Hukumar Inshora ta Kasa (National Insurance Commission) zuwa Hukumar Kula da Harkokin Inshora (Insurance Regulatory Commission).
Ya ce kudirin zai taimaka wajen samar da cikakken tsarin doka don tsara dokoki da sa-ido kan dukkan nau’ukan harkokin inshora a Najeriya.
Ya jaddada cewa hakan zai bai wa bangaren inshora damar yin gasa cikin nasara a matakin duniya, tare da inganta karfin gasar Najeriya da bangaren inshora a fagen kasa da kasa.
Ya yi kira ga Majalisar Dattawa da ta yi la’akari da rahoton tare da amincewa da Kudirin Kafa Hukumar Kula da Harkokin Inshora na shekarar 2026.
A nasa tsokacin, Sanata Osita Izunaso (APC, Imo) ya ce idan aka amince da kudirin, bangaren inshora zai samu ingantaccen tsarin dokoki da kulawa mai karfi, kamar yadda ake yi a bangaren kasuwar jari ta hanyar Dokar Zuba Jari da Tsaron Kadarori (Investments and Securities Act) ta 2025.
Sanata Aminu Abbas (APC, Adamawa) ya ce amincewa da kudirin zai kara dawo da kwarin gwiwa ga masu gudanar da harkokin inshora, tare da tabbatar da fadada ayyukan bangaren a tsakanin al’umma.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, a jawabinsa bayan amincewa da kudirin, ya gode wa kwamitin bisa gagarumar gudummawar da ya bayar kan kudirin.
Sanata Akpabio ya ce ta hanyar amincewa da kudirin, Majalisar Dattawa za ta bar bangaren inshora a cikin yanayi mafi kyau fiye da yadda ta same shi.
Ya taya Majalisar Dattawa murna bisa nasarar amincewa da kudirin.
Aisha.Yahaya, Lagos



