Shugaban Ahmadiyya Ya Gabatar Da Rahoton Duniya Na Ci Gaba Ta Shekarar 2026

Shugaban Musulmin Ahmadiyya na duniya, Hazrat Mirza Masroor Ahmad (Khalifatul Masih na V), ya gabatar da rahoton ci gaban shekara-shekara na kungiyar Ahmadiyya ta shekarar 2026.
An gabatar da rahoton ne a taron Musulunci na shekara-shekara (Jalsa Salana) karo na 60 na kungiyar Ahmadiyya ta kasar Birtaniya, a Hadeeqatul Mahdi, Alton, Hampshire, Birtaniya, inda mahalarta da baki sama da 50,000 suka halarta.
KARANTA KUMA: Najeriya ta tura tawaga zuwa taron Musulunci na Ahmadiyya na duniya
A cewar shugaban Ahmadiyya na duniya, wannan rahoto mai kyau ya kunshi batutuwan yada addinin Musulunci ta hanyar fassara Alkur’ani Mai Girma zuwa harsunan gida da na duniya, gina sabbin masallatai, bude sabbin cibiyoyin Ahmadiyya a sassan duniya, rarraba littattafan addinin Musulunci, da kuma karuwar sabbin mambobi a cikin kungiyar.
Kididdiga
Shugaban Ahmadiyya na duniya, Hazrat Masroor Ahmad, ya kara da cewa “sakon Musuluncin Ahmadiyya na ci gaba da isa ko’ina a fadin duniya ta hanyar imani, sadaukarwa, da addu’o’i.” Daga sabbin masallatai da gidajen mishan zuwa miliyoyin littattafan da aka rarraba da kuma daruruwan dubban mutanen da suka shiga kungiyar, wadannan ba kawai lambobi ba ne; alamomi ne na albarkar Allah.”
Aisha.Yahaya, Lagos



