NSCIA Ta Gudanar Da Addu’ar Kasa Baki Daya Domin Tabbatar Da Zaman Lafiya A Najeriya.

Majalisar Kololuwa ta Harkokin Addinin Musulunci na Najeriya (NSCIA) su gudanar da addu’ar kasa a Babban Masallacin Kasa da ke Abuja, domin neman taimakon Allah wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro, ci gaban tattalin arziki, da kuma shugabanci na gari a Najeriya.
Sakataren Janar na NSCIA, wanda kuma shi ne tsohon Shugaban Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’o’i (JAMB), Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana cewa taron ya kasance nauyi ne na addini da na kasa, ba wai wani taron siyasa ba.
Oloyede ya bayyana cewa Babban Masallacin Kasa ya samar da dandamali ga Musulmi daga bangarori daban-daban na siyasa domin su hada kai wajen yi wa kasa da shugabancinta addu’a.
KARANTA KUMA: Sarkin Musulmi ya yi kira da a ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya

Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi addu’ar neman shiri daga Allah ga shugabannin ƙasar da kuma duk waɗanda ke shiga harkokin siyasa, ba tare da la’akari da jam’iyyarsu ta siyasa ba. Haka kuma, yayin da yake jawabi, Limamin Babban Masallacin Ƙasa kuma Mataimakin Mashawarcin Shari’a na ƙasa na ƙungiyar NSCIA, Imam Harun Mohammed Eze, ya bayyana cewa an shirya wannan addu’a ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙungiyar NSCIA kuma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar.
Imam Eze ya bayyana cewa an yi addu’ar neman taimakon Allah kan ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta, ciki har da matsalar tsaro, talauci, yunwa da sauran matsalolin zamantakewa da tattalin arziki.
Ya ce an kuma yi addu’a domin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima, ‘yan Majalisar Dokoki ta ƙasa, ɓangaren shari’a da sauran shugabannin siyasa.

Malamin ya jaddada muhimmancin gaskiya, sadaukarwa, da neman shiriya daga Allah ga wadanda aka dora wa nauyin kula da harkokin jama’a.
Imam Eze ya bayyana cewa, halartar da malaman addinin Musulunci da shugabannin addini daga yankuna shida na siyasar kasar suka yi, ya nuna hadin kan Musulmi da kuma kudirin hadin gwiwa wajen ci gaban Najeriya.
A cikin nasiharsa, wani Imam na Babban Masallacin Kasa, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da ba da muhimmanci ga ilimi, zaman lafiya, tsaro, ci gaban tattalin arziki, da kuma jin dadin iyalai da al’ummomi.
Malamin sun jaddada muhimmancin gaskiya, sadaukarwa, da neman shiriya daga Allah ga wadanda aka dora wa nauyin kula da harkokin jama’a. Imam Eze ya bayyana cewa, halartar da malaman addinin Musulunci da shugabannin addini daga yankuna shida na siyasar kasar suka yi, ya nuna hadin kan Musulmi da kuma kudirin hadin gwiwa wajen ci gaban Najeriya.
A cikin nasiharsa, wani Imam na Babban Masallacin Kasa, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da ba da muhimmanci ga ilimi, zaman lafiya, tsaro, ci gaban tattalin arziki, da kuma jin dadin iyalai da al’ummomi.
Manyan malamai da shugabannin addinin Musulunci sun halarci taron addu’ar, ciki har da wakilan Babban Limamin Offa da na jihohin Delta, Imo da Borno; Muftin Ilorin; Sarkin Malamin Jihar Sokoto; Shugaban Kungiyar Limamai da Malamai ta Kudu maso Yammacin Najeriya; da kuma Wakilin Musulmi na yankin Yarbawa.
An gudanar da addu’ar ne domin murnar cika shekaru 66 da Najeriya ta samu ‘yancin kai a ranar 1 ga watan Oktoba, inda ta hada kan malamai, manyan limamai, shugabannin gargajiya, da wakilan al’ummar Musulmi daga yankuna shida na siyasar kasar.

NSCIA ta bayyana cewa addu’ar ta kasa ta bai wa Musulmi damar sake mika Najeriya da shugabancinta ga Allah, tare da neman shiriyar Ubangiji da taimakonsa wajen tunkarar kalubalen da kasar ke fuskanta.
NSCIA/Aisha.Yahaya, Lagos



