Zaben 2027: Shugaban Majalisar Dattawa Akpabio Ya Yi Alkawarin Kuri’u Miliyan Biyu Ga Shugaba Tinubu

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio Gwamna Umo Eno da sarakunan gargajiya a Jihar Akwa Ibom sun sake jaddada goyon bayansu ga Shugaba Bola Tinubu. Akpabio ya yi alkawarin cewa jihar za ta samar da kuri’u sama da miliyan biyu ga Shugaban a babban zaben shekarar 2027.
Shugabannin sun bayyana matsayinsu ne a wani liyafar cin abinci da aka shirya domin girmama Tinubu inda suka yi tsokaci kan manufofin gwamnatinsa suka amince da alkawuran da ya dauka na bunkasa Jihar Akwa Ibom tare da bayyana amincewarsu ga jagorancinsa.
Akpabio ya bayyana Tinubu a matsayin shugaba mai gaskiya hangen nesa da kuma kwarewa wajen aiki wanda manufofinsa ke sake tsara Nijeriya.
“Malam Shugaba kai mutum ne mai gaskiya mai gaskiyar magana mai tunani kuma mai cika alkawari da aiki. A Jihar Akwa Ibom muna kokarin koyi da kai” in ji shi.

Yayin da yake tuno lokacin da yake matashi yana aiki a Legas a lokacin da Tinubu ke Gwamna Akpabio ya ce ya yi sha’awar tsarin ci gaban da Tinubu ya gabatar kuma ya kuduri aniyar koyi da salon jagorancinsa idan ya samu damar mulki.
Ya ce Tinubu ya kawo wannan hangen nesa zuwa matakin kasa inda ya bayyana cewa “Nijeriya na canzawa saboda Shugaba Tinubu yana kan karagar mulki.”
Da yake ambaton cire tallafin man fetur gina hanyar da ta bi ta bakin teku da kuma kokarin fadada tushen tattalin arziki Akpabio ya bayyana Tinubu a matsayin shugaba mai cika alkawura.
“Wannan Shugaba ba ya karya shi mutum ne mai cika alkawari” in ji shi.
Ya bai wa Tinubu tabbacin cewa Majalisar Dokokin Tarayya za ta ci gaba da ba shi goyon baya, yana mai cewa “A karkashin jagorancinka za mu ci gaba da ganin ci gaba.”
Akpabio ya kuma bayyana cewa gwamnonin yankin Kudu-maso-Kudu sun goyi bayan Tinubu saboda sun fahimci hangen nesansa na kawo ci gaba.
“Har zuwa lokacin da za ka kammala wa’adinka a shekarar 2031 ba za ka taba kasancewa kai kadai ba” in ji shi ga Shugaban kafin ya kara da cewa “Wannan jiha za ta ba ka kuri’u sama da miliyan biyu.”
Gwamna Umo Eno ya nuna godiyarsa ga Shugaba Tinubu saboda cika alkawarin da ya yi na ziyartar Jihar Akwa Ibom da kuma amincewa da aikin gina tashar jiragen ruwa mai zurfi ta Ibom (Ibom Deep Seaport).

Ya tuna cewa duk da rade-radin da jama’a suka yi game da ziyarar Shugaban ya ba shi tabbacin cewa “Zan cika alkawarin.” Eno ya kuma bayyana cewa sakin kudade da Gwamnatin Tarayya ta yi zuwa jihohi ya bai wa gwamnatinsa damar aiwatar da ayyukan ci gaba.
Ya kawo misali da wurin shakatawa na ‘Arise Palm Resort’ wanda aka gina a kan wani yanki mai fadin hekta 73 da ke fama da mummunar zaizayar kasa wadda a da ta yi barazana ga Gidan Gwamnati a matsayin misalin sauyin da aka samu sakamakon daukar matakai masu karfi da inganci.
“Muna danganta dukkan wadannan ayyuka a gare ku. Saboda haka muna gode muku. Muna gode muku” in ji shi.
A yayin gabatar da jawabin godiya, Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Akwa Ibom wanda kuma shi ne ‘Oku Ibom Ibibio Ntenyin Dr. Solomon Etuk ya nuna godiya ga Tinubu bisa amincewa da aikin gina tashar jiragen ruwa mai zurfi ta Ibom (Ibom Deep Seaport) inda ya ce al’ummar yankin sun yi farin ciki da samun amincewar fara aikin.

Ya bayyana goyon bayan masarautu da shugabannin gargajiya ga burin Shugaban Kasa tare da yin kira da a kara bai wa ‘yan asalin jihar Akwa Ibom mukamai a gwamnatin tarayya.
Taron cin abincin ya samu halartar Uwargidan Shugaban Kasa matar Mataimakin Shugaban Kasa Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai gwamnonin yankin Kudu-maso-Kudu ‘yan majalisa na tarayya da na jihohi ministoci mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar Akwa Ibom da sauran shugabannin siyasa



