Siyasa

Zaben 2027: INEC Ta Fitar Da Jadawalin Yakin Neman Zabe Na Hukuma.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da jadawalin yakin neman zabe na hukuma domin Babban Zaben 2027, bisa tanade-tanaden Dokar Zabe ta 2026.

Ga cikakken bayanin jadawalin yakin neman zaben, kamar yadda yake a cikin sanarwar da Shugaban INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN), ya sanya wa hannu kuma aka wallafa a shafin yanar gizon hukumar na www.inecnigeria.org:

Zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Dokoki ta Kasa; Fara yakin neman zabe: Talata, 19 ga Agusta, 2026. Kammala yakin neman zabe: Juma’a, 15 ga Janairu, 2027, sa’o’i 24 kafin ranar zaben da aka tsara gudanarwa a ranar 16 ga Janairu, 2027.

Zaben Gwamna da na Majalisar Dokoki ta Jiha; Fara yakin neman zabe: Laraba, 9 ga Satumba, 2026. Kammala yakin neman zabe: Juma’a, 5 ga Fabrairu, 2027, sa’o’i 24 kafin ranar zaben da aka tsara gudanarwa a ranar 6 ga Fabrairu, 2027.

KARANTA KUMA: INEC ta sake jaddada kudirinta na gudanar da ingantaccen zabe a 2027

Muhimman Tanade-Tanaden Dokar Zabe Ta 2026

Ana iya fara yakin neman zaben siyasa ne kawai kwana 150 kafin ranar zabe. Dole ne dukkan ayyukan yakin neman zabe su kare sa’o’i 24 kafin ranar kada kuri’a.

An haramta wa jam’iyyun siyasa, ‘yan takara, da magoya bayansu fara yakin neman zabe kafin ranakun da aka amince da su a hukumance; kuma INEC ta bayyana cewa duk wanda ya karya wannan doka zai iya fuskantar matakan ladabtarwa da suka dace.

Wannan sabon jadawalin ya yi daidai da Dokar Zabe ta 2026 kuma ya maye gurbin jadawalin zaben da INEC ta gabatar a baya.

Saboda haka, ana sa ran jam’iyyun siyasa da ‘yan takara za su fara yakin neman zabe a bainar jama’a—ciki har da tarukan siyasa, tallace-tallace a kafofin yada labarai, tuntubar masu zabe, da kuma hada kan jama’a a matakin tushe—tun daga ranar 19 ga Agusta, 2026 domin zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Dokoki ta Kasa, da kuma daga ranar 9 ga Satumba, 2026 domin zaben Gwamna da na Majalisar Dokoki ta Jiha.

Ana kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su bi jadawalin da aka amince da shi dari-bisa-dari domin tabbatar da gudanar da zabe cikin lumana, gaskiya, da kuma bin doka.

 

Aisha.Yahaya, Lagos

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button