Siyasa

Atiku Ya Yaba Wa Mazauna Jihar Sokoto Ya Yi Alkawarin Inganta Tsaro Da Harkar Noma

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) Alhaji Atiku Abubakar ya yabi al’ummar jihar Sokoto bisa fitowarsu da yawa domin tarbarsa yayin ziyarar da ya kai jihar.

Atiku Abubakar ya yi alkawarin cewa idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa gwamnatinsa za ta ba da fifiko ga tsaron kasa ta sake bude iyakokin kasar na kasa ta saukaka harkokin aikin Hajji tare da inganta ci gaban fannin noma.

Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su zabi jam’iyyar ADC yana mai bukatar masu kada kuri’a su kasance a rumfunan zaben su domin tabbatar da cewa an kirga kuri’unsu yadda ya kamata.

Haka zalika abokin takararsa Rotimi Amaechi ya yi kira ga ‘yan Najeriya da kada su bari wasu mutane su yi amfani da su wajen haifar da tashin hankali ko dagula zaman lafiyar jama’a.

KARANTA KUMA: http://Atiku ya isa Sokoto domin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar ADC

Shugaban jam’iyyar ADC na kasa wanda kuma tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya ne Sanata David Mark ya bayyana cewa “Jam’iyyar ta kuduri aniyar ceto ‘yan Najeriya daga kalubalen da kasar ke fuskanta.”

Sauran fitattun ‘yan siyasa da suka halarci taron sun hada da shugaban kungiyar ‘Atikulate Group Barrister Abba Hikima mai fafutukar kare hakkin dan adam Hajiya Naja’atu Muhammad Sakataren jam’iyyar ADC na kasa Abdulrauf Aregbesola da kuma shugaban matasan jam’iyyar na kasa Rufai Balarabe.

Haka kuma tsohon Sanata Dino Melaye Sanata Aminu Waziri Tambuwal da sauran fitattun ‘yan siyasar jam’iyyar ADC daga sassan kasar daban-daban sun halarci taron.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button