Minista Ya Yi Hasashen Shugaba Tinubu Zai Samu Kashi 85 Na kuri’un Yankin Arewa Ta Tsakiya.

Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Najeriya, Mohammed Idris, ya bayyana kwarin gwiwar cewa Shugaba Bola Tinubu zai samu kashi 85 na kuri’u a yankin Arewa ta Tsakiya a babban zaben shekarar 2027.
Idris ya yi wannan hasashen ne a babban taron kungiyar ‘North-Central Grassroots Mobilisation Network’ da aka gudanar a Lafia Jihar Nasarawa inda shugabannin siyasa da magoya baya suka bayyana goyon bayansu ga sake zaben Shugaba Tinubu da Mataimakin Shugaba Kashim Shettima.
Taron ya bai wa mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) damar bayyana nasarorin da gwamnatin ta cimma tare da yin alkawarin kara kaimi wajen wayar da kan jama’a a matakin tushe a duk fadin yankin.

KARANTA KUMA: 2027: Shugaba Tinubu Ya Amince da Jadawalin Yaƙin Neman Zaɓen Jam’iyyar APC
Idris ya bayyana wannan mataki na nuna goyon baya a matsayin shawara ta haɗin gwiwa da kuma ta son rai daga gwamnoni ministoci da shugabannin siyasa na yankin Arewa ta Tsakiya inda ya nuna kwarin gwiwar cewa ci gaba da goyon bayan gwamnatin zai kawo ƙarin amfanin dimokuradiyya ga yankin.
“Muna yanke shawara ta haɗin gwiwa a matsayinmu na duka, tare da dukkan gwamnoni, ministoci, da shugabannin siyasa na yankin Arewa ta Tsakiya. Za mu zaɓi Shugaba Bola Ahmed Tinubu,” in ji shi.
Yaƙin Neman Zaɓe Mai Mayar Da Hankali Kan Batutuwa
Ministan ya yi kira ga magoya bayan dukkan jam’iyyun siyasa da su mayar da hankali kan yaƙin neman zaɓe mai dogaro da batutuwa tare da guje wa tashin hankali yayin da ake shirin gudanar da zaɓen shekarar 2027.
“Saƙon da muke da shi shi ne ya kamata kowa ya gudanar da yaƙin neman zaɓe bisa batutuwa. Babu tashin hankali babu rikici babu faɗa. Idan kana da abin da za ka gabatar ba sai ka yi faɗa ba,” in ji Idris.
Ya jaddada cewa jam’iyyar APC tana da nasarorin da za ta gabatar wa ‘yan Najeriya kuma ya yi alkawarin cewa gwamnatin za ta yi ƙarin ayyuka idan aka sake zaɓen ta.
“Dukkanmu muna nan. Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu kashi 85 na ƙuri’un yankin Arewa ta Tsakiya. Sauran kuma za a bar musu kashi 15 ne su raba a tsakaninsu,” ya ƙara da cewa.
Haka kuma Ministan Jiha mai kula da Harkokin Noma Aliyu Abdullahi ya bayyana cewa za a ci gaba da shirye-shiryen tattara goyon bayan jama’a a matakin tushe har zuwa ranar zaɓe.
“Mutanenmu sun shirya tsaf kuma za su ci gaba da wannan shiri da wayar da kan jama’a har sai ranar da kuri’unmu za su yi magana,” in ji shi
Abdullahi ya bayyana cewa an ba batun samar da isasshen abinci muhimmanci na dindindin a karkashin jagorancin Tinubu inda ya kara da cewa ana ci gaba da kokarin daidaita tsarin samar da abinci da kuma magance matsalar tsadar jigilar kayan gona.
Ya bayyana tsadar jigila a matsayin babban abin da ke shafar farashin abinci tare da nuna cewa ana sa ran inganta hanyoyin sadarwa zai rage kudin da ake kashewa wajen jigilar kayan amfanin gona daga gonaki zuwa kasuwanni.
“Wani lokacin ana samun abinci mai rahusa, amma kudin jigilarsa yana zama mai tsada sosai. Ana kuma gyara hanyoyinmu domin a rika jigilar abinci kan farashi mai sauki,” in ji shi.
Ministan Harkokin Waje na Kasa Jakada Sola Enikanolaiye, ya bayyana wannan gangamin a matsayin farkon wani babban shiri na tattara goyon baya ga Tinubu a yankin da ma wuraren da suka wuce haka.
Ya ce za a fadada yakin neman zaben zuwa sauran jihohi tare da jaddada muhimmancin ci gaba da kuma dorewar shirye-shiryen gwamnati.
Hakazalika, Ministar Harkokin Mata, Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta bayyana cewa gyare-gyare da shirye-shiryen tallafawa al’umma da gwamnatin ke aiwatarwa sun ba da fifiko ga masu rauni, ciki har da mata da yara.
Ta bayyana kwarin gwiwa kan damar jam’iyyar APC ta samun nasara a zabe inda ta ce zaben shekarar 2027 zai bai wa ‘yan Najeriya damar tantance ayyukan gwamnatin.
Wannan gangami na daga cikin kokarin da shugabanni da magoya bayan jam’iyyar APC a yankin Arewa ta Tsakiya ke yi na karfafa goyon baya ga Shugaba Tinubu da Mataimakin Shugaba Shettima gabanin babban zaben shekarar 2027.
Aisha.Yahaya, Lagos



