Wasanni

Harry Kane Na Shirin Zama Ɗan Wasa Mafi Yawan Buga Wa Ingila

Kyaftin din tawagar Ingila Harry Kane zai kafa tarihi a ranar Alhamis yayin da zai buga wasansa na 126 a matakin kasa da kasa inda zai zama dan wasan kwallon kafa na maza da ya fi kowa yawan buga wa kasar wasa a karawar da za su yi da Croatia a gasar UEFA Nations League a filin wasa na Wembley.

Dan wasan gaba na Bayern Munich mai shekaru 33 zai zarce tsohon mai tsaron gida Peter Shilton wanda ya rike tarihin da wasanni 125 tun shekarar 1989.

Kafin fara wasan Kane zai gabatar da kyautar Ballon d’Or da ya lashe a watan da ya gabata ga magoya bayan Ingila a wani biki na musamman inda ake sa ran Shilton ma zai kasance cikin wadanda za su halarci girmamawar.

Yayin da yake magana gabanin wannan muhimmin lokaci Kane ya bayyana nasarar a matsayin daya daga cikin manyan abubuwan da ya taba cimmawa a rayuwarsa ta kwallon kafa inda ya danganta dorewarsa a mataki mafi girma ga sadaukarwa aiki tukuru da kuma daidaito a kan aiki.

“Tabbas wannan yana daya daga cikin manyan nasarorin da na taba samu a rayuwata ta kwallon kafa. Yana nuna dorewa a mataki mafi girma kuma cimma yawan wasannin da na buga shaida ce ta sadaukarwa” in ji Kane ga manema labarai a ranar Laraba.

KARANTA KUMA: Harry Kane Ya Lashe Ballon d’Or na Farko Bayan Kakar Wasa ta Kafa Tarihi

Dan wasan gaban ya riga ya kafa kansa a matsayin wanda ya fi kowa zura kwallaye a tarihin tawagar Ingila inda ya zarce tarihin Wayne Rooney na kwallaye 53 a shekarar 2023. Tun daga lokacin ya kara yawan kwallayen da ya ci a matakin kasa da kasa zuwa 91 wanda hakan ya kara karfafa matsayinsa a cikin fitattun ‘yan wasan kasar.

Kocin tawagar Ingila Thomas Tuchel ya yabi jagorancin Kane da tasirinsa inda ya kwatanta shi a matsayin “kyaftin din da ya dace kuma shugaba mai zama abin koyi”. Ya kuma yabi yadda dan wasan ke iya daidaita salon wasansa tare da kara nuna basira yayin da yake samun karin gogewa.

Kane wanda ya ci kwallaye 73 a wasanni 65 da ya buga wa Bayern Munich da Ingila a kakar wasan da ta gabata ya bayyana cewa har yanzu yana da kwarin gwiwar cimma karin nasarori inda ya sanya burin cin kwallaye 100 a matakin kasa da kasa a matsayin daya daga cikin manufofinsa na gaba.

Sai dai ya bayyana cewa lashe babban kofi na kasa da kasa tare da Ingila shi ne babban burinsa inda ya amince cewa kawo karshen dogon lokacin da kasar ta shafe tana jira kafin ta sake lashe kofi shi ne babban mafarkinsa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button