Habasha Ta Zargi Eritrea Sudan Da Masar Da Tallafawa Kungiyoyi Masu Dauke Da Makamai.

Habasha ta zargi Eritrea Sudan da Masar da goyon bayan kungiyoyin ‘yan tawaye masu dauke da makamai a daidai lokacin da ake ci gaba da sabon rikici a arewacin kasar tare da fargabar yiwuwar shigar kasashen yankin baki daya cikin lamarin.
Babban hafsan sojin Ethiopia Field Marshal Birhanu Jula ne ya yi wadannan zarge-zargen a karshen makon da ya gabata inda ya danganta rashin zaman lafiyar kasar da wadanda ya kira “makiyan Ethiopia na tarihi da na yanzu.”
Jula ya zargi Eritrea da zama hanyar sadarwa tsakanin kasashen waje ciki har da Sudan da Masarda kuma kungiyoyin ‘yan tawaye masu dauke da makamai da ke gudanar da ayyukansu a cikin Ethiopia.
Bai gabatar da hujjojin tabbatar da wadannan zarge-zargen ba.
Wadannan zarge-zargen sun zo ne a daidai lokacin da rikici ya tsananta a arewacin Ethiopia musamman a yankunan Tigray Amhara da Afar bayan barkewar sabon rikici tsakanin sojojin gwamnatin tarayya da kungiyar Tigray People’s Liberation Front (TPLF) da kawayenta.
Kasashen Eritrea Sudan da Masar sun musanta wadannan zarge-zargen.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Masar Nader Zaki ya ce: “Manufar harkokin wajen Masar ta ginu ne kan mutunta ikon mallakar kasa hadin kai da kuma mutuncin iyakokin kasashe tare da rashin tsoma baki cikin harkokin cikin gidansu.”
Zaki ya kara da cewa: “Masar ta ci gaba da bin dokokin kasa da kasa da Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kuma ta yi watsi da duk wani mataki da zai iya kawo barazana ga tsaro da kwanciyar hankalin yankin.”
Tsohon shugaban sashen kula da morali na sojin Masar, Manjo Janar Samir Farag shi ma ya bayyana zarge-zargen da ake yi wa Masar a matsayin ‘marasa tushe’ yana mai cewa “ba manufar kasar ba ce ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashen yankin.”
Sojojin Sudan sun yi watsi da zarge-zargen tare da bayyana su a matsayin marasa tushe, inda su ma suka zargi Ethiopia da goyon bayan rundunar Rapid Support Forces (RSF) rundunar da ba ta gwamnati ba wadda ke yaki da sojojin Sudan tun shekarar 2023. Ethiopia ta musanta wannan zargi.
Rikice-rikice a yankin
Dangantaka tsakanin Ethiopia da wadannan kasashe uku ta yi tsami sakamakon dadaddun rikice-rikice.
Ethiopia da Masar na ci gaba da samun sabani kan madatsar ruwa ta Grand Ethiopian Renaissance Dam da ke kan kogin Blue Nile yayin da tashin hankali tsakanin Ethiopia da Sudan ya karu sakamakon yakin basasar da ke ci gaba a Sudan.
Dangantaka tsakanin Ethiopia da Eritrea ta lalace tun bayan rikicin Tigray na shekarun 2020–2022 lokacin da sojojin Eritrea suka yi yaki tare da sojojin gwamnatin tarayyar Ethiopia domin yakar kungiyar TPLF. Sabon fadan ya haifar da damuwa game da rashin kwanciyar hankali a yankin kusurwar Afirka inda tashin hankali kan tsaro yakin basasar Sudan da kuma damar shiga Tekun Bahar Maliya suka kasance masu muhimmanci a yankin.



