AfirkaKiwon Lafiya

Adadin Mutanen Da Suka kamu Da Cutar Ebola A Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo Ya Haura 11,000 Ya Yin Da Mutane 5,387 Suka Mutu.

Adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo (DR Congo) ya kai 11,042 yayin da aka samu rahoton mutuwar mutane 5,387 a cewar bayanan gwamnati da aka fitar ranar Talata.

An sanar da barkewar cutar wadda nau’in kwayar cutar Ebola mai wuyar samu da ake kira ‘Bundibugyo‘ ke haifarwa a tsakiyar watan Mayu kuma ta shafi larduna takwas cikin larduna 26 na kasar.

Nau’in na ‘Bundibugyo‘ ba shi da rigakafin da aka amince da shi ko kuma takamaiman magani lamarin da ke haifar da damuwa game da kokarin dakile yaduwar cutar.

Wannan barkewar cutar ita ce ta biyu mafi girma kuma mafi muni a tarihi bayan annobar Ebola da ta faru a Yammacin Afirka tsakanin shekarar 2014 zuwa 2016 wadda ta shafi mutane sama da 28,600 kuma ta yi sanadin mutuwar mutane fiye da 11,000.

KARANTA KUMA: Barkewar Ebola a Kongo ta Zarce Mutane 10,000 da Aka Tabbatar Sun Kamu

Jami’an kiwon lafiya sun bayyana cewa jinkirin gano cutar rikice-rikicen da ke faruwa da kuma karancin karfin tsarin kiwon lafiya sun taimaka wajen yaduwar kwayar cutar cikin sauri yayin da mutane da yawa suka mutu a wajen cibiyoyin da aka ware domin bayar da kulawa.

Haka kuma an samu rahoton kasancewar cutar a yankunan Gabas Tsakiya da Yammacin Afirka wanda hakan ya sa wannan barkewar ta zama ta Ebola mafi yaduwa a fadin nahiyar Afirka baki daya.

 

 

Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button