Najeriya

Uwargidan Shugaban Kasa Ta Taya Yara Murna A Ranar Yara Ta Duniya

Yayin da Najeriya ke shiga tare da sauran kasashen duniya wajen gudanar da bikin Ranar Yara ta Duniya na wannan shekarar Uwargidan Shugaban Kasa Oluremi Tinubu ta bayyana cewa dole ne a bai wa yara damar rayuwa koyo da kuma jin dadin dukkan abubuwan da rayuwa ke bayarwa.

A cikin sakon da ta fitar domin tunawa da wannan rana Mrs. Tinubu ta jaddada bukatar kare yara daga hatsarorin zamani da ci gaban fasaha ke jefa su a ciki.

Ta ce: “A yau a yayin bikin Ranar Yara ta Duniya na shekarar 2026 mai taken ‘Ranata. Hakkokina. Makomarta bari mu tabbatar da cewa an bai wa kowane yaro damar koyo girma rayuwa cikin aminci da kuma cimma cikakken karfinsu na zama abin da za su iya zama.

“A cikin wannan duniya mai saurin sauyi alkawarin kare yaranmu ya kamata ya kunshi kare su daga hatsarorin zamani kamar fasahar basirar dan-adam (AI) da ba ta da tsari da kuma illolin jarabar kafofin sada zumunta na yanar gizo tare da tabbatar da cewa an kare lafiyar kwakwalwarsu da walwalarsu a duniyar dijital. Ya kamata mu sadaukar da kanmu wajen kare dukkan yaranmu. Barka da Ranar Yara ta Duniya.”

Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 20 ga watan Nuwamba a kowace shekara domin inganta hakkokin yara wayar da kan jama’a game da jin dadinsu da kuma karfafa hadin kan kasa da kasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button