Najeriya

Uwargidan Shugaban Kasa Ta Kaddamar Da Hedikwatar Yakin Neman Zabe Na ‘Gida-Gida’

Uwargidan Shugaban Najeriya Oluremi Tinubu ta bayyana cewa kasar tana kan turbar da ta dace don samun cikakken farfadowar tattalin arziki da ci gaba mai dorewa inda ta jaddada cewa amincewar masu zuba jari kan tattalin arzikin kasar ya inganta sosai.

Ta bayyana hakan ne yayin kaddamar da hedikwatar kungiyar ‘President Bola Tinubu Door-to-Door Movement’ (Kungiyar Ziyarar Gida-gida ta Shugaba Bola Tinubu) a birnin Abuja.

Uwargidan Shugaban kasar ta bukaci mambobin kungiyar da kada su takaita aikin nasu ga ziyartar gidaje kawai sai dai su isar da sakon bege tabbaci da kuma wadata ga kowa.

Ta ce: “Yakin neman zabe ta hanyar ziyartar gidaje na daya daga cikin muhimman hanyoyin hulda ta hakika da al’umma. Wannan yana ba mu damar sauraron damuwar iyalai fahimtar burin matasanmu girmama hikimar dattawanmu da kuma koyo kai tsaye daga mata wadanda su ne ginshikin gidajenmu da al’ummarmu baki daya.

“Yayin da muke gudanar da wannan aiki mai daraja ya kamata mu tuna cewa ingantaccen aikin wayar da kan jama’a ya wuce ziyartar kofofin gidaje kawai. Sakonmu dole ne ya kasance mai cike da bege zaman lafiya hadin kai da ci gaba musamman ma ci gaban da gwamnatin Shugaba Tinubu ta samu kawo yanzu.”

KARANTA KUMA: Mataimakin Shugaban Kasa Ya Yi Ikirarin Cewa Yankin Kudu-Maso-Kudu Na Goyon Bayan Shugaba Tinubu

Madam Tinubu ta yaba wa shugabanni da mambobin kungiyar bisa ziyartar jihohi 14 na tarayya, inda ta bukace su da su ci gaba da wannan kaimi yayin da yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ya fara a hukumance.

“Ga mambobin kungiyar ‘PBAT Door-to-Door Movement’ ina kira a gare ku da ku kusanci kowace al’umma cikin lumana ku tunkari kowane mutum cikin girmamawa kuma ku tuna cewa kowane dan Najeriya yana da hakkin a saurare shi kuma a daraja shi ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasar da yake ciki ba.

“Mu lashe zukatansu da kuri’unsu ta hanyar karfin sakonmu wato: ‘Sabon Bege’ (Renewed Hope) ‘Tsarin Tarayya na Hakika’ (True Federalism) da kuma ‘Wadata ga Kowa’ (Shared Prosperity)” cewar ta.

Alƙawarin Samun Ci gaba

A cikin jawabinsa Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su nuna amincewa ga gwamnati tare da ba da tabbacin cewa za a samu ci gaba a ƙasar baki ɗaya.

“Saƙon da nake son isarwa shi ne cewa akwai bege bege ya zo kuma bege yana nan daram” in ji shi.

Haka kuma yayin da yake jawabi a wajen taron Gwamnan Jihar Delta Sheriff Oborevwori ya bayyana a fili cewa jihohi na samun sauƙi da ci gaba a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu. Ya yi nuni da cewa yanayin kuɗaɗen jihohi ya inganta ta yadda ba a bin ma’aikata bashin albashi kuma ana biyan ‘yan kwangila kuɗaɗensu a kan lokaci.

Shugaban ƙungiyar ‘PBAT Door-to-Door Movement’ ya ba da tabbacin cewa ƙungiyar za ta kai wannan saƙo zuwa kowane lungu da saƙo na ƙasar domin tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen watan Janairun 2027.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button