Shugaba Tinubu Ya Yi Kira Ga Likitocin Kasashen Waje Da Su Dawo Gida

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga kwararrun likitocin Najeriya mazauna kasashen waje da su dawo gida domin bayar da gudunmawa wajen ci gaban kasa.
Shugaban ya yi wannan kiran ne yayin da ya karbi bakuncin wakilan kungiyoyin likitocin Najeriya mazauna kasashen waje karkashin jagorancin Shugabar Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje (NiDCOM) Misis Abike Dabiri-Erewa a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ci gaba da jajircewa wajen cimma manufofin shirin ‘Renewed Hope Agenda’ (Shirin Sabon Fatan Ci Gaba) ta hanyar samar da yanayi mai kyau da zai bai wa ‘yan Najeriya damar samun ci gaba da kuma bayar da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban kasa.
KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje su goyi bayan Tinubu
“Abin farin ciki ne matuka ganin kuna dawowa domin cimma babban burinku na taimaka wa kasarku da kuma biyan bukatun al’ummarmu. Kudurinku na sadaukar da kai ga dan-adam wani bangare ne na muhimmiyar alkawarin da kuka dauka a rayuwa. Ina yi muku duka godiya. Na taba yin irin wannan tafiyar. Yanzu ina gida, kuma zan iya gaya muku cewa babu inda ya kai gida dadi.
“Yaranku za su dauki ginshikin wannan kasa a matsayin nasu kuma muna matukar kokari ne domin tabbatar da cewa makomar kasar ta kasance tasu; hakika gudummawar da kuke bayarwa ta hanyar dawowa tana da matukar muhimmanci da daraja” in ji Shugaban.
Shugaban Najeriya ya tabbatar wa tawagar cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da manufofin da ke da nufin inganta rayuwar ‘yan kasa, inda ya bayyana cewa talauci abu ne da ba za a amince da shi ba kuma yana kawo cikas ga ci gaban kasa.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa Najeriya tana da karfin da za ta iya kawar da talauci da rashin ci gaba ta hanyar hadin gwiwa, inganta ilimi, kyautata harkokin kiwon lafiya, ci gaba mai dorewa da kuma wadata ta fuskar tattalin arziki.
“Talauci da rashin ci gaba kalubale ne ga nahiyar Afirka. Amma a matsayinka na dan Najeriya, me kake gani? Wannan ita ce zuciyar Afirka; hanya mafi kyau ta nuna muku hakan ita ce ta hanyar sadaukar da kaina ga tsarina na ‘Sabon Fatan Rayuwa’ (Renewed Hope), domin tabbatar da fatan ‘yan Najeriya na samun ingantaccen muhalli da ingantaccen ilimi da ci gaba da wadata da kuma fatanku na ganin wannan yanki na nahiyar ya canza zuwa yanayi mai kyau da maraba da mutane. Domin ku ma ku samu damar bayar da gudummawa wata rana.
“Ana bukatar kudurce-kudurce masu karfi da kuma tsayawa kan manufa. Talauci ba abu ne da ya kamata a amince da shi ba. Ba za mu amince da shi ba. Za mu yaki shi Za mu kawo wadata. Za mu kula da al’ummarmu” in ji Shugaban.
Ya ce tafiyar dimokuradiyyar Najeriya har yanzu tana cikin matakin ci gaba amma kasar tana kan turbar samun kwanciyar hankali mai dorewa da wadata da kuma farfado da kasa.
“Idan ka dubi tafiyar har zuwa yanzu har yanzu muna matakin farko. Muna cikin lokacin kuruciya. Idan ka kwatanta da shekaru 250 na dimokuradiyyar Amurka da kuma shekaru aru-aru na tsarin mulkin Birtaniya” in ji shi.
Shugaban ya sake jaddada kudirinsa na karfafa tsarin mulkin dimokuradiyya yana mai cewa bambance-bambancen da ke Najeriya babban dukiyar kasa ce da ya kamata a yi amfani da ita wajen samar da ci gaba mai dorewa.
“Abin da zan iya yi muku alkawari shi ne, duk da kalubale da sauye-sauyen da ke tattare da dimokuradiyya bambance-bambancenmu suna kara bunkasa ta fuskar kwarewa a aiki kabila da addini kuma muna aiki tukuru don tabbatar da kwanciyar hankali” in ji Shugaba Tinubu.
LADAN NASIDI



