Gwamnatin Najeriya Na Gudanar Da Bincike Kan Mutuwar Mutane 37 A Hannun Hukumar NSCDC.

Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamiti mai zaman kansa mai mutane 10 domin gudanar da bincike kan rahoton mutuwar mutane 37 da ke tsare a hannun hukumar tsaro ta NSCDC a Jihar Neja wadanda ake zargi da hannu cikin harkar hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.
An dora wa kwamitin alhakin gano ko su waye wadanda suka mutu tare da bincikar yanayin da ya shafi kama su tsare su da kuma mutuwar tasu haka kuma za su tantance ko akwai wanda ke da alhaki hannu sakaci ko kuma aikata ba daidai ba dangane da wannan lamari.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ga manema labarai na fadar shugaban kasa a ranar Asabar Ministan Harkokin Cikin Gida Olubunmi Tunji-Ojo ya sanar da kafa kwamitin biyo bayan umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na a gudanar da cikakken bincike mai gaskiya da kuma rashin cikas kan lamarin mutuwar mutanen.
KARANTA KUMA: Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin bincike kan mutuwar mutane a wurin tsarewa a Minna – Voice of Nigeria
Tunji-Ojo ya kuma bayar da umarnin dakatar da dukkan jami’an da ke da hannu a lamarin har sai an kammala binciken wadannan sun hada da Kwamandan NSCDC na Jihar Neja da wasu jami’ai 20 da ma’aikatar ta fitar da sunayensu da mukamansu.
Ga Jerin Sunayen Jami’an da aka dakatar:
1. SC Usman Isah Ndamaka – O/C Station Guard (Shugaban masu gadin tashar)
2. ASCI Hassan Mohammed – Station Guard (Mai gadin tashar)
3. CCA Bala Mohammed – Station Guard (Mai gadin tashar)
4. CSC Oluwadare Sunday – Arresting Officer / O/C Investigation (Jami’in da ya yi kama / Shugaban sashen bincike)
5. DCC Obafemi Elvis – Arresting Officer (Jami’in da ya yi kama)
6. CSC Annas Shitto Lamino – Arresting Officer (Jami’in da ya yi kama)
7. DCC Philip Ajayi – HOD INT/INV (Shugaban sashen tattara bayanai da bincike)
8. ACC Barr. Stephen Tsado – Shugaban Sashen Shari’a (O/C Legal)
9. ASCI Alhassan Mohammed – Jami’in Aiki na Rana da Dare
10. IC Abdullahi Sale – Aikin Tsaro
11. IC Mohammed Sonfada – Aikin Tsaro
12. CAI Liman Abubakar – Aikin Tsaro
13. CAI Bala Usman – Aikin Tsaro
14. IC Mohammed Jiya – Aikin Tsaro
15. DSC Isah Suleiman – Aikin Tsaro
16. CAI Ahmed Wushishi – Aikin Tsaro
17. IC Sale Adamu – Aikin Tsaro
18. IC Haruna Mohammed – Aikin Tsaro
19. ASCI Aliyu Sallah – Aikin Tsaro
20. CAI Isah Sanusi – Aikin Tsaro
Yayin da yake bayyana mutuwar a matsayin abin takaici da damuwa sosai ministan ya ce ya zama wajibi ga gwamnatin Najeriya ta bai wa iyalan wadanda suka rasu da kuma ‘yan Najeriya cikakken bayani mai gamsarwa game da lamarin.
Kwamitin yana karkashin jagorancin Mataimakin Darakta Janar na Ma’aikatar Ayyukan Jiha Jonathan Kure yayin da tsohon Darakta Janar na Makarantar Shari’a ta Najeriya Farfesa Isa Hayatu Chiroma SAN zai yi aiki a matsayin sakatare.
Sauran membobin sun hada da Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Hosea Hassan Karma mai ritaya Farfesa a fannin ilimin tarihi kuma tsohon Babban Daraktan Lafiya na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin Olayinka Buhari wakilan Majalisar Masarautar Minna da Gwamnatin Jihar Neja Sakataren Kasa na Kungiyar Masu Hako Ma’adinai ta Najeriya Liman Sulaiman lauya kuma mai fafutukar kare hakkin dan adam Deji Adeyanju Mrs Zainab Suleiman Okino na Jaridar Blueprint da kuma mai sharhi kan harkokin jama’a Dr. George Agbakahi.
An kuma umarci kwamitin da ya ba da shawarar daukar matakin da ya dace kan duk wanda aka samu da laifi ya tantance yiwuwar diyya idan ya dace sannan ya gabatar da matakan hana sake afkuwar lamarin.
A cewar ministan kwamitin zai iya hada kwararru masu dacewa samun damar kayan aiki da takardu da suka dace ziyartar wuraren da abin ya shafa da kuma karbar takardu daga jama’a.
Tunji-Ojo ya umarci shugabannin NSCDC da duk jami’an da abin ya shafa da su ba da cikakken haɗin kai ga binciken tare da tabbatar da cewa an adana bayanai da shaidun da suka shafi lamarin kuma an bai wa masu bincike damar yin hakan.
Ya yi gargaɗin cewa duk wani yunƙuri na lalata ko ɓoye shaida tsoratar da shaidu ko hana binciken za a ɗauke shi a matsayin babban laifi.
Kwamitin yana da makonni biyu don kammala bincikensa da kuma gabatar da rahotonsa ga ministan.
Tunji-Ojo ya kuma yi ta’aziyya ga iyalan mamatan tare da roƙon a kwantar da hankali yayin da ake ci gaba da binciken.
Shugaba Tinubu ya ba da umarnin a gudanar da bincike kan kama mutane yanayin tsare su kulawar lafiya da aka bayar da kuma abubuwan da suka haifar da mutuwar.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis 17 ga Satumba wanda ya shafi mutanen da Hukumar NSCDC ta Jihar Neja ta tsare bisa zargin hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.
Daga baya Ministan Harkokin Cikin Gida ya jagoranci tawagar Gwamnatin Najeriya zuwa Jihar Neja kan mutuwar wanda aka ruwaito cewa ya shafi ma’aikatan hakar ma’adinai 37.



