Najeriya

An Buɗe Taron Shekara-shekara Na Musuluncin Ahmadiyya Karo Na 60 A Birtaniya

 

Daga tutar Ahmadiyya

Daga Tuta A Taron Jalsa Salana Na Birtaniya attached flag

Shugaban Al’ummar Musulmi ta Ahmadiyya na duniya, Hazrat Mirza Masroor Ahmad (Khalifatul Masih na V), ne ya bayyana bude taron Jalsa Salana na Burtaniya na shekarar 2026, wanda shi ne karo na 60 na wannan taro na shekara-shekara.

An fara bikin bude taron ne da gudanar da Sallar Juma’a da kuma daga tuta a filin taron Hadeeqatul Mahdi da ke Alton, a yankin Hampshire na kasar Burtaniya.

Sanin Allah Da Jin Tsoronsa

Shugaban kungiyar Ahmadiyya ta Musulmi, a jawabinsa na farko, ya yi kira ga Musulmi da mambobin kungiyar Ahmadiyya da su rungumi ingantattun koyarwar Musulunci tare da kiyaye tsoron Allah a dukkan harkokinsu. Ya kuma bukaci kowa da ya yi sadaukarwa ta musamman ga Allah tare da yin addu’a ta gaske domin samun alherin duniya da na lahira.

Rangadin Wajen Taron

Kafin gudanar da bikin bude taron, shugaban kungiyar Ahmadiyya ya ziyarci wurin da ake gudanar da taron Jalsa Salana a kasar Birtaniya a ranar Alhamis Da Ta Gabata domin duba shirye-shirye, tare da yi wa masu aikin sa-kai da ke aiki dare da rana jawabi.

Shugaban kungiyar Ahmadiyya ya ziyarci wuraren da ake girki—ciki har da sashin yin burodin ‘roti’, wurin yanka nama, wurin wanke tukwane, da kuma sito—inda ya yi nazari dalla-dalla kan yadda wadannan sassa ke gudanar da ayyukansu tare da tattaunawa da ma’aikatan da ke bakin aiki.

Daga nan, ya zagaya wuraren baje kolin ayyuka daban-daban, wadanda suka hada da Humanity First, The Review of Religions, True Islam UK, International Association of Ahmadi Architects and Engineers (IAAAE), ITQA, Ahmadiyya Archive & Research Centre, da kuma Al Hakam—wanda a wannan shekarar ya baje kolin samfurin garin Qadian.

Kullum Ka Kasance Mai Ladabi Da kyawawan Halaye.

Bayan haka, Hazrat Khalifatul Masih na V ya hau dandamali domin gabatar da takaitaccen jawabi ga masu aikin sa-kai, inda ya bukace su da su kasance masu ladabi da kyawawan halaye, kamar yadda suka saba yi a shekarun baya.

A cewarsa, “aikin da aka dora wa mutum wani lokacin yana iya zama mai nauyi har ma ya sa mutum ya rasa natsuwa, amma ya kamata masu aikin sa-kai su kasance masu ladabi da fara’a a kowane lokaci. Ko a sassan da ke bukatar tsananin natsuwa da tsari—kamar sashen kula da da’a—ya kamata masu aikin sa-kai su nuna kyakkyawan hali tare da yi wa baƙi jagora cikin taushin hali”.

Jaddada Matakan Kiyaye Hadarin Gobara

Ya shawarci masu aikin sa-kai da su yi taka-tsantsan sosai domin guje wa afkuwar gobara ta bazata, la’akari da yadda yanayi ya yi tsananin bushewa kuma ciyawa ke da saurin kama wuta. Ya yi nuni da cewa, yin girki a wurin kasuwar na iya haifar da hadarin gobara idan ba a dauki matakan kariya da suka dace ba. Saboda haka, bai kamata a dauki duk wani hadari da ba dole ba, kuma dole ne dukkan masu aikin sa-kai su kasance masu sa ido tare da bin dukkan ka’idojin kariya daga gobara.

Dole Ne A Dauki Batun Tsaro Da Muhimmanci.

Yayin da yake lura da yadda ake samun tsananin kyamar Musulmi a halin yanzu, Hazrat Khalifatul Masih ya bayyana cewa akwai babban bukatar ba da kulawa ta musamman wajen tabbatar da tsaron dukkan wurin da ake gudanar da taron Jalsa.

Ya yi addu’ar Allah Ya ba dukkan masu aikin sa-kai ikon gudanar da ayyukansu ta hanya mafi kyau, sannan ya jagoranci kowa wajen yin addu’a a cikin shiru.

Taron Shekara-shekara Na Ahmadiyya Na 2026

Shugaban Ahmadiyya ya kuma ziyarci sashin mata, tare da shafe lokaci mai tsawo a harabar MTA International, inda ya gana da masu aikin sa-kai da dama.

 

Aisha.Yahaya, Lagos

 

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button