APC ta musanta takardar INEC Ta Bogi Game Da Sake Zaɓen Shugaba Tinubu

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta musanta wata wasika da ake zargin cewa Shugaban Jam’iyyar na Kasa Farfesa Nentawe Yilwatda ya rubuta wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) inda yake neman goyon bayan hukumar domin sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027.
A cikin wata sanarwa Mataimaki na Musamman ga Shugaban Jam’iyyar na Kasa kan Harkokin Yada Labarai da Dabarun Sadarwa Abimbola Tooki ya bayyana wasikar wacce ba ta dauke da sa hannu ba a matsayin takardar bogi da aka kirkira domin bata sunan shugabancin jam’iyyar.
Ya bayyana cewa wasikar ba ta fito daga Farfesa Yilwatda ko ofishinsa ba.
Jam’iyyar ta siffanta takardar a matsayin kirkirar karya ta mugun nufi da kuma yunkuri na ganganci da nufin raunana mutuncin shugabancinta da kuma tsarin zabe na kasa.
Ta ce rashin sa hannu ko wata alama ta tabbatar da sahihancin takardar ya nuna cewa yunkuri ne na yaudarar jama’a da haifar da cece-kuce da kuma bata sunan Shugaban Jam’iyyar na Kasa.
Jam’iyyar APC ta kuma ce wasikar da ake zargin ta saba wa ka’idojin sadarwa da tsarin gudanarwa da aka kafa tana mai dagewa cewa ba za a iya fitar da wata takarda mai muhimmanci a wajen hanyoyin gwamnati ba.
Jam’iyyar ta kalubalanci wadanda ke bayan takardar da su fito su bayar da shaida mai inganci kan ikirarinsu a maimakon boyewa a boye don yada labaran karya.
Ta sake jaddada kudirinta na gudanar da zabe cikin lumana da gaskiya da ‘yanci da adalci a shekarar 2027 tana mai jaddada cewa tana girmama ‘yancin INEC da ‘yancin ‘yan Najeriya na zabar shugabanninsu cikin ‘yanci.
KARANTA KUMA: Kamfanin Lauyoyi Ya Bukaci INEC Da Ta Karfafa Gaskiyar Zabe
APC ta ce Shugaba Tinubu ya ci gaba da karfafa wa ‘yan Najeriya da suka cancanta gwiwa su sami Katin Zabe na Dindindin su kuma shiga cikin tsarin zabe yana mai bayyana hakan a matsayin shaida ta amincewarsa da ka’idojin dimokuradiyya.
Ta bukaci ‘yan Najeriya da kafofin watsa labarai da su yi watsi da wasikar da ake zargin tana mai dagewa cewa nasarar zaben za ta dogara ne akan tarihinta hangen nesanta da kuma goyon bayan masu kada kuri’a.
Ladan Masidi.



