Portugal Ta Yi Bincike Kan Amfani Da Tushen Jirgin Sama Na Lajes

Masu gabatar da kara na kasar Portugal sun fara gudanar da bincike kan halaccin matakin da gwamnatin tsakiya-dama ta dauka na bai wa Amurka damar amfani da sansanin sojin saman Lajes da ke tsibiran Azores a lokacin rikicin da ake fama da shi da Iran.
An fara binciken ne bayan wata korafi da ‘yan jam’iyyar adawa ta Left Bloc suka shigar, inda suka yi ikirarin cewa wannan izini ya saba wa dokokin kasa da kasa.
Wata tsohuwar yarjejeniyar tsaro ta bai wa Amurka damar amfani da sansanin ba tare da neman izini ba a lokacin zaman lafiya, amma tana bukatar amincewar Portugal da zarar an fara rikici ko yaki.
Portugal ta amince da wasu jiragen Amurka su bi ta Lajes domin wucewa, sabanin makwabciyarta Spain. Wannan mataki ya jawo suka daga jam’iyyun adawa masu ra’ayin hagu tare da haifar da muhawarar siyasa kan rawar da Lisbon ke takawa a ayyukan da ke da alaka da rikicin.
KARANTA KUMA: Iran ta harba makamai masu linzami kan sansanin da Amurka ke amfani da shi a Jordan
A cikin wata sanarwa, ofishin Babban Mai Gabatar da Kara ya bayyana cewa an fara binciken ne bayan korafin da ‘yan jam’iyyar Left Bloc suka shigar, amma ba su bayar da karin bayani ba.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Portugal ta ki cewa komai game da lamarin.
A watan Afrilu, jam’iyyar Left Bloc ta bukaci masu gabatar da kara su binciki yadda Amurka ke amfani da sansanin, inda ta bayyana hakan a matsayin “mummunan take dokokin kasa da kasa.”
Ministan Harkokin Waje Paulo Rangel ya yi watsi da wannan ikirari, yana mai cewa Portugal ba ta shiga cikin rikicin ba kuma amfani da sansanin ya yi daidai da dokokin kasa da kasa.
Ya ce Lisbon ta amince da zirga-zirgar jiragen ne kawai bayan ta samu tabbaci daga Washington cewa duk wani aiki zai kasance na kare kai ne, mai matukar muhimmanci, kuma ya dace da yanayin, sannan zai takaita ne kawai ga wuraren da sojoji ke hari.
Dangane da ka’idar bin doka ta Portugal, dole ne masu gabatar da kara su binciki zargin aikata ba daidai ba idan akwai isassun dalilai na yin hakan. Sansanin sojin saman Lajes, wanda ke tsibiran Azores na Portugal, muhimmin wurin wucewa ne ga sojojin Amurka bisa yarjejeniyar tsaro ta bangarorin biyu da aka kulla tun shekarar 1951.
Sansanin yana daukar sashen sojin saman Amurka mai lamba 65 (65th Air Base Wing) kuma yana tallafawa ayyukan Amurka, NATO da sauran kawayenta.
Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos



