Kenya – Mutane Biyu Sun Mutu Sakamakon Ebola Ta Kuma Tabbatar Da Kamuwar Mutane Tara Da Cutar.

Kenya ta samu rahoton mutuwa ta biyu sakamakon cutar Ebola tare da tabbatar da mutane tara da suka kamu da cutar. A halin yanzu kungiyar Red Cross ta Kenya tana horar da ma’aikatanta kan yadda ake gudanar da jana’iza cikin aminci da mutunci domin rage barazanar yaduwar cutar.
Kungiyar Red Cross ta Kenya ta bayyana cewa kula da gawarwakin wadanda suka mutu sakamakon Ebola da kuma binne su na daya daga cikin matakan da ke dauke da babban hadarin yaduwar cutar. Saboda haka kungiyar ta shirya horon tunatarwa da kuma gwaje-gwajen aiki na zahiri ga tawagocinta da ke birnin Nairobi.
Shugaban sashen kula da gaggawa na kiwon lafiyar jama’a a kungiyar Red Cross ta Kenya Dr. Paul Olale ya bayyana cewa an dora wa kungiyar alhakin kula da jana’izar wadanda suka mutu sakamakon cutar Ebola.
“A zahiri muna gudanar da wasu gwaje-gwajen aiki ne. A kasar nan an ba mu amanar kula da jana’izar wadanda suka mutu sanadiyyar cutar Ebola,” in ji shi.
Dr. Olale ya bayyana cewa an shirya wadannan atisaye ne domin tabbatar da cewa tawagocin kungiyar a shirye suke su dauki mataki cikin aminci a duk lokacin da aka samu bullar cutar.
“Muna kokarin tunatar da tawagarnmu yadda ake gudanar da jana’iza cikin aminci da mutunci domin tabbatar da cewa suna a shirye a kowane lokaci idan bukatar hakan ta taso,” in ji shi.
Mutum na farko da aka tabbatar ya kamu da cutar a Kenya wani mutum ne da ya yi tafiya daga Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo zuwa Nairobi inda ya rasu a birnin a ranar 5 ga watan Oktoba.
A cewar Ma’aikatar Lafiya mutum na biyu da ya rasu mace ce mai shekaru 65 wacce ta mutu a ranar Juma’a fa ta gabata. Ta kasance ‘yar uwa ta kusa ga mutum na farko da ya kamu da cutar kuma sun yi mu’amala kai tsaye da juna.
Ma’aikatar ta bayyana cewa ta gano mutane 135 da ka iya zama sun yi mu’amala da mutum na farko da ya kamu da cutar kuma an sanya su a killace (quarantine).
Dr. Olale ya ce dukkan mutane tara da aka tabbatar sun kamu da cutar suna da alaka da mutum na farko da ya kamu da ita.
“Abubuwan a bayyane suke; idan aka bi jerin yadda cutar ta yadu daga mutum na farko za a ga cewa wadannan ‘yan uwa ne na kusa wadanda suka yi mu’amala da shi a lokuta daban-daban,” in ji shi.
Ya kara da cewa ba a samu rahoton sabbin masu dauke da cutar a wajen birnin Nairobi ba yayin da sauran mutane bakwai da aka tabbatar suna dauke da cutar ke samun kulawa a cibiyoyin killace marasa lafiya guda biyu.
Tun bayan tabbatar da bullar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo a watan Mayu mutane sama da 4,000 ne suka mutu a nahiyar Afirka inda aka samu rahoton bullar cutar a kasashe hudu a nahiyar.
Labaran Afirka/Aisha.Yahaya, Lagos



