Mataimakin Shugaban Kasa Shettima Ya Jagoranci Taron Majalisar Tattalin Arziki Ta Kasa

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ne ke jagorantar taron Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) ta yanar gizo domin duba yanayin tattalin arzikin kasar da kuma nazarin matakan da za a dauka don bunkasa ci gaban tattalin arzikin.
Taron wanda ya fara da karfe 10:40 na agogon GMT Mataimakin Shugaban Kasar ne ke jagorantar sa daga ofishinsa da ke fadar shugaban kasa (Presidential Villa) a Abuja.
Daga cikin wadanda ke halartar taron akwai Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki Atiku Bagudu da kuma Ministan Aikin Gona da Tsaron Abinci Abubakar Kyari.
Gwamnoni ma suna shiga taron ne ta yanar gizo daga ofisoshinsu daban-daban a fadin kasar.
Majalisar tana gudanar da taro duk wata domin duba yanayin tattalin arziki da kuma nazarin manufofi ko matakan da za su inganta ayyukan tattalin arziki.
Cikakkun bayanai daga baya.



