Ghana Ta Karbi Bakuncin Taro Kan Batun Samar Da Kudade Ga Hukumar Tarayyar Afirka

Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka (AU) Mahmoud Ali Youssouf ya isa birnin Accra na kasar Ghana domin halartar taro na musamman na 27 na Majalisar Zartarwa ta kungiyar.
Taron wanda aka tsara gudanarwa a ranar Juma’a 13 ga watan Nuwamba zai mayar da hankali ne kan batun samar da kudade ga kungiyar.
Taron zai bai wa ministocin harkokin waje da wakilan kasashe mambobi damar duba hanyoyin karfafa ‘yancin tafiyar da harkokin kudi na kungiyar tare da rage dogaro da kudade daga wajen nahiyar.
Tattaunawar za ta mayar da hankali kan tara albarkatu daga cikin nahiyar inganta tsarin gudanar da kasafin kudi da kuma samar da ingantattun hanyoyin samun kudade masu dorewa domin tallafawa shirye-shirye da muhimman ayyukan Tarayyar Afirka.
Ayyukan Samar da Zaman Lafiya da Asusun Zaman Lafiya
Ana sa ran tattauna batun samar da kudade ga ayyukan samar da zaman lafiya da kuma karfafa Asusun Zaman Lafiya yayin da kungiyar ke kokarin samun isassun albarkatu domin tunkarar kalubalen tsaro da bukatun ci gaba a nahiyar.
KARANTA KUMA: Ghana Ta Bayyana Shirin Zuba Jari Na Dala Biliyan 10 Domin Bunkasa Tattalin Arziki
Wannan taro na musamman wani mataki ne a cikin kokarin da Tarayyar Afirka ke yi na tabbatar da dorewar samar da kudade karfafa ‘yancin gudanarwa na kungiyar da kuma inganta karfinta na aiwatar da shawarwarin da hukumominta masu gudanarwa suka yanke.
Ta hanyar wannan mataki kungiyar na da burin ganin cewa an samar da kudade domin gudanar da muhimman ayyukanta daga cikin nahiyar Afirka wanda hakan zai zama babban ginshiki na tabbatar da ‘yancin kai da kuma ingancin ayyukanta.



