Afirka Ta Kudu Ta Kama Mutane Tara Bisa Zargin Shiga Ayyukan Sojan Haya

‘Yan sandan Afirka ta Kudu sun kama ‘yan ƙasashen waje guda tara da ake zargi da yunkurin tafiya Rasha don shiga yaƙin da ke tsakanin Rasha da Ukraine bisa zargin karya dokokin ƙasar da ke kula da tallafin sojojin ƙasashen waje.
‘Yan sanda sun ce an kama waɗanda ake zargin, ‘yan shekaru 20 zuwa 26 a makare a filin jirgin saman O.R. Tambo International da kuma wani otel da ke kusa da yankin Bruma na Johannesburg.
Kakakin ‘yan sanda Kanar Katlego Mogale ya ce kama mutanen ya biyo bayan wani bincike da ya shafi Interpol da hukumomin tsaro na cikin gida da na ƙasashen waje.
An ruwaito cewa waɗanda ake zargin suna shirin shiga jiragen sama zuwa Rasha lokacin da jami’an tsaro suka shiga tsakani. ‘Yan sanda ba su bayyana ƙasashensu ba ko kuma sun nuna ɓangaren rikicin da ake zargin suna da niyyar shiga.
Ana sa ran waɗanda ake zargin su tara za su bayyana a gaban Kotun Majistare ta Kempton Park bisa zargin da ake yi musu na karya Dokar Taimakon Sojojin Ƙasashen Waje ta Afirka ta Kudu. ‘Yan sanda ba su sanar da ranar da za su bayyana a kotu ba.
KARANTA KUMA: Shiga tsakani na Amurka a yakin Rasha da Ukraine ya tsaya cak Duk da sabbin tattaunawa
Dokar ta haramta ayyukan ‘yan amshin shata kuma ta tsara tallafin soja ga bangarorin da ke da hannu a rikice-rikicen kasashen waj gami da daukar ma’aikata da horarwa. Takardun sun kuma shafi ‘yan kasashen waje da ke aiki a cikin Afirka ta Kudu.
Kamen ya zo ne a daidai lokacin da ake nuna damuwa kan daukar ‘yan Afirka aiki domin shiga rikicin Rasha da Yukiren inda rahotanni ke cewa ana zargin wasu mutane da yin alkawuran aikin farar hula da kuma fa’idodi masu kyau.
Wani bincike da Code for Africa wata kungiya mai zaman kanta ta aikin jarida da fasaha, ta gano gidajen yanar gizo yankuna da kuma bayanan kafofin sada zumunta guda 289 da ake zargin ana amfani da su wajen jawo hankalin ma’aikata ta hanyar tallace-tallacen da ba su dace ba da kuma alkawuran samun fa’idodi masu yawa, a cewar Cibiyar Nazarin Tsaro.
Afirka ta Kudu ta kuma taimaka wajen mayar da ‘yan kasarta da dama da ta ce an jawo su cikin rikicin.
AP/LADAN



