Najeriya

NYSC Ta Kayyade Ranar Taron Ga Masu Yi Wa ƙasa Hidima Na ‘B’ Sashe Na II Shekarar 2026.

Hukumar Kula da Shirin Yi wa Kasa Hidima ta Matasa (NYSC) ta kayyade ranar Laraba, 5 ga watan Agusta, 2026, a matsayin ranar fara shirin horarwa na rukunin ‘Batch B Stream II’ na shekarar 2026 a dukkan sansanonin horarwa da ke fadin kasar nan.

A cikin wata sanarwa, Daraktar yada labarai da hulda da jama’a ta hukumar NYSC, Caroline Embu, ta bayyana cewa shirin horarwar, wanda zai dauki tsawon makonni uku, za a gudanar da shi ne a lokaci guda a dukkan jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT), inda zai zo karshe a ranar Talata, 25 ga watan Agusta, 2026.

Hukumar ta kuma sanar da cewa an riga an sanya lambobin kiran shiga shirin (Call-up Numbers) a shafukan yanar gizo na masu shirin fara hidimar, yayin da za a fitar da takardun kiran shiga shirin (Call-up Letters) nan ba da jimawa ba.

KARANTA KUMA: Za a fara shirin horarwar NYSC na rukunin ‘Batch A’ a ranar 21 ga watan Janairu

Darakta-Janar na NYSC, Birgediya Janar Olakunle Nafiu, ya taya dukkan matasan da aka kira domin fara hidimar kasa ta rukunin ‘Batch B Stream II’ na shekarar 2026 murna bisa nasarar kammala karatunsu a manyan makarantu, na cikin gida da na wajen Najeriya.

Ya kuma yi kira gare su da su yi tafiya cikin aminci zuwa sansanonin horarwarsu, su guji yin tafiya da daddare, tare da bin dukkan ka’idojin tafiye-tafiye da na tsaro yadda ya kamata a duk tsawon tafiyarsu.

 

Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button