EAC Ta Dauki Matakin Hanzarta Hadewar Kasuwannin Jari Na Yankin.

Kungiyar Kasashen Gabashin Afirka (EAC) ta sake farfado da Karamin Kwamitin Kasuwannin Jari wanda ke karkashin Kwamitin Kasuwannin Jari Inshora da Fansho (CMIPC).
Ana sa ran wannan mataki zai hanzarta aiwatar da shirye-shiryen hadewar kasuwannin jari na yankin domin shirye-shiryen kafa Kungiyar Kudi ta Gabashin Afirka.
Rahoton da kamfanin APO Group ya fitar a madadin Kungiyar EAC ya bayyana cewa an cimma wannan kudiri ne yayin taron Karamin Kwamitin Kasuwannin Jari na kwana uku wanda aka gudanar daga ranar 15 zuwa 17 ga watan Satumbar 2026.
Taron ya hada manyan jami’ai masu gudanarwa da kuma kwararrun wakilai daga hukumomin musayar hannun jari hukumomin kula da kasuwannin jari da tsare-tsaren hannun jari da kuma cibiyoyin ajiiyar hannun jari na kasa (Central Securities Depositories) daga kasashen da ke cikin kungiyar EAC.



