Hare-Haren RSF Sun Sa Dubban Mutane Tserewa Daga Yankin Blue Nile Na Sudan

Kungiyar sojojin sa-kai ta Sudan mai suna Rapid Support Forces (RSF) ta yi ikirarin cewa ta kwace ikon yankin Geissan gaba daya wanda ke yankin Blue Nile kusa da iyakar kasar Habasha yayin da rundunar sojin kasar ta musanta hakan tare da cewa har yanzu ana ci gaba da fada.
Rundunar sojin Sudan ta bayyana cewa har yanzu tana rike da ikon wani muhimmin sansanin soja a yankin lamarin da ya saba wa ikirarin da RSF ta yi na cewa ta kwace garin.
A cewar Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM) fadan ya sa kimanin mutane 2,500 barin gidajensu inda wasu fararen hula suka tsallaka zuwa kasar Habasha makwabciya.
An rawaito cewa an kai harin ne a lokacin girbi inda ake zargin RSF da sace amfanin gona da kuma kwashe kayayyaki a babban kasuwar Geissan.
KARANTA KUMA: Sudan ta tura sojoji zuwa iyakar Habasha
Matsayin garin na da matukar muhimmanci ta fuskar dabarun soja inda zai iya bai wa RSF damar samun karin iko kan hanyoyin samar da kayayyaki da kuma damar shiga yankunan da ke kusa da madatsar ruwa ta Roseires.
Haka kuma gwamnatin Sudan ta zargi Habasha da taimakawa wajen isar da tallafin soja daga Hadaddiyar Daular Larabawa zuwa ga kungiyar RSF. Kasar Habasha ta musanta wadannan zarge-zargen.
Masana sun bayyana cewa harin na iya zama wani yunkuri na rarraba karfin rundunar sojin kasar yayin da take samun nasarori a wasu sassan kasar.
Africa/LADAN NASIDI



