Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Ta Umarci ‘Yan Kasa Su Zuba Jari A Bangaren Hakar Ma’adinai

Jamhuriyar Demokradiyyar Congo za ta fara aiwatar da wata doka da aka dade ana jinkirtawa, wadda ke bukatar kamfanonin hakar ma’adinai su bai wa ‘yan kasar damar mallakar hannun jari, tun daga ranar 31 ga watan Yuli.
Ma’aikatar ma’adinai ta bayyana hakan ne duk da damuwar da wasu daga cikin manyan kamfanonin hakar jan karfe da cobalt na duniya suka nuna game da tasirin dokar a fannin.
A baya, kamfanonin hakar ma’adinai a Congo—kasar da ta fi kowacce samar da cobalt a duniya kuma ta biyu wajen samar da jan karfe—sun yi kokarin ganin an dage aiwatar da dokar ta shekarar 2018. Dokar ta bukaci kamfanonin su mika kashi 10 na hannun jarinsu ga ‘yan kasar Congo, ciki har da kashi 5 da aka kebe domin ma’aikata. Babu kamfanin da ya bi dokar har yanzu, saboda wasu tambayoyi da ba a warware su ba game da yadda za a aiwatar da ita.
A watan Janairu, gwamnatin Kinshasa ta umurci kamfanoni—ciki har da Glencore, Ivanhoe Mines, da kamfanonin kasar Sin irin su CMOC da Huayou Cobalt—su tabbatar sun bi dokar kafin karshen watan Yuli ko kuma su fuskanci takunkumi, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Ma’aikatar ma’adinai ta sake jaddada wa’adin ranar 31 ga watan Yuli a wani sako da ta wallafa a shafin X ranar Talata da ta gabata, bayan tattaunawa da kamfanonin hakar ma’adinai game da wata doka ta musamman da ke bayyana yadda za a aiwatar da ka’idar.
KARANTA KUMA: Ebola: Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da dala miliyan 60 a matsayin tallafin gaggawa ga DRC
“Dole ne kamfanonin hakar ma’adinai su bi tanade-tanaden doka game da shigar ‘yan kasar Congo cikin tsarin mallakar hannun jarinsu,” in ji ma’aikatar.
Bangarorin sun amince cewa ya kamata a sanya hannu kan dokar bayan an yi wasu gyare-gyare na fasaha, kamar yadda sakon a shafin X ya nuna. An kafa wani kwamiti na musamman domin kammala wadannan gyare-gyaren.
Sakon bai yi cikakken bayani game da gyare-gyaren ba. Haka kuma ba a san irin takunkumin da kamfanonin za su iya fuskanta ba idan ba su bi dokar ba.
Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos



