Libya Ta Kama Mutane Biyar Kan Harin Jiragen Sama Marasa Matuki A Kan Matatar Mai

Hukumomi a yammacin Libya sun kama mutane biyar dangane da hare-haren jiragen sama marasa matuki da aka kai kwanan nan kan wani babban cibiyar samar da makamashi.
Gwamnati ta ce kama mutanen ya fallasa wani “babban makirci” kuma ta bayyana hare-haren a matsayin wani bangare na wani shiri na hadin gwiwa.
Hukumomin sun ce kungiyar na cikin “sashin lalata” wanda shi ma ya shirya kai hari kan tashar samar da wutar lantarki a kudancin Tripoli da kuma wasu muhimman wurare.
Sun ce ‘yan kasashen waje suna cikin wadanda ake zargi amma ba su bayar da karin bayani ba.
A watan Agusta, wani babban ma’ajiyar mai a Zawiya ya kama da wuta yayin wani hari da jiragen sama marasa matuki suka kai kan wani babban cibiyar mai kusa da Tripoli in ji kamfanin mai na kasar Libya NOC.
Ma’ajiyar tana cikin matatar mai ta biyu mafi girma a Libya wacce ke da karfin tace ganga 120,000 a kowace rana. Wasu hare-haren jiragen sama marasa matuki sun biyo baya a ginin Zawiya wanda ke da nisan kilomita 45 yamma da Tripoli.
A ranar Alhamis, an dakile wani hari kan tankunan mai a wajen Tripoli in ji NOC.
KARANTA KUMA: Gwamnatocin Libya masu adawa da juna sun cimma yarjejeniya kan jadawalin gudanar da zabe
Libya ce ke da mafi yawan arzikin man fetur a nahiyar Afirka. Sai dai kasar na fama da tashe-tashen hankali da rashin kwanciyar hankali tun bayan hambarar da gwamnatin Muammar Gaddafi a shekarar 2011.
A halin yanzu akwai gwamnatoci biyu da ke fafutukar ganin sun kama ragamar mulki gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita a birnin Tripoli karkashin jagorancin Firayim Minista Abdulhamid Dbeibah da kuma wata gwamnati mai adawa da ita a yankin gabashin kasar wadda kwamandan soji Khalifa Haftar ke mara wa baya.
Ladan Nasidi.



