Najeriya

An Kaddamar Da Sabbin Rukunin Sojoji A Jihohi Hudu — Shugaba Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Rundunar Sojin Najeriya ta kaddamar da sabbin rukunin sojoji a jihohin Zamfara, Kebbi, Oyo, da Osun, domin kusantar da sojoji ga al’ummomin da ke cikin hadari tare da karfafa martani cikin gaggawa ga barazanar tsaro.

Shugaban kasa ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi da ta gabata hanyar wani sako a shafinsa na hukuma a dandalin X, wato @OfficialABAT, yayin da yake bayyana matakan da gwamnatinsa ke dauka don inganta karfin aiki da walwalar Rundunar Soji.

Shugaba Tinubu ya kuma bayyana cewa GwamnatTarayya na hanzarta gina sabbin barikin soji da wuraren ajiye kayan aiki a jihohin Abuja, Ekiti, Ebonyi da Kogi, yayin da aka riga aka kammala aikin da ake yi a jihar Osun.

“A wannan makon, Rundunar Sojin Najeriya (@HQNigerianArmy) ta fara gudanar da ayyuka a sabbin sansanoni a jihohin Zamfara, Kebbi, Oyo da Osun. Yanzu sojojinmu sun fi kusanci da al’ummomin da ke cikin hadari a wadannan yankuna, lamarin da ke kara mana karfin daukar mataki cikin gaggawa da kuma tsauri a duk lokacin da aka yi barazana ga al’ummarmu.

“Muna kuma hanzarta gina sabbin barikin soji da wuraren ajiye kayan aiki a Abuja, Ekiti, Ebonyi da Kogi, yayin da na jihar Osun ya riga ya kammala. Yayin da muke bukatar karin kwazo daga maza da matan da ke sanye da kayan soji, dole ne mu kara kokari wajen tallafa musu da iyalansu.

Kowane aikin tura sojoji zuwa fagen aiki sadaukarwa ce da iyali ke yi,” in ji Shugaba Tinubu.

Ya jaddada cewa dole ne a biya karuwar nauyin da ke kan sojoji maza da mata da karin tallafi a gare su da iyalansu, inda ya lura cewa tura sojoji aiki na bukatar sadaukarwa daga iyalansu ma.

“A ‘yan kwanakin nan, sojoji maza da mata na Rundunar Soji sun bayyana irin tasirin da karin albashin da aka yi kwanan nan ke da shi a gare su da iyalansu. Ina farin cikin ganin cewa yana kawo sauyi mai kyau,” in ji Shugaba Tinubu.

Shugaban ya kuma yi nuni da tasirin karin albashin da aka yi wa jami’an Rundunar Soji, inda ya ce ra’ayoyin da sojojin ke bayarwa sun nuna cewa karin yana kawo sauyi mai kyau a rayuwarsu da ta iyalansu.

“Yayin da Rundunar Sojinmu ke tsaron Najeriya, aikina a matsayin Babban Kwamandan Sojoji shi ne tabbatar da cewa suna da kayan aiki da tallafin da ake bukata don gudanar da ayyukansu, tare da tabbatar da cewa Najeriya na tsaye sosai tare da iyalan da ke jiran dawowarsu gida.”

Shugaba Tinubu ya sake jaddada kudirin gwamnatin Najeriya na ci gaba da tallafawa jami’an soji da iyalan da ke ba su goyon baya yayin da suke yi wa kasa hidima.

 

 

Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button