UNESCO Ta Soki Rashin Hukunta Masu Aikata Laifuka Kan ‘Yan Jarida

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da al’adu wato UNESCO ta bayyana cewa rashin hukunta wadanda ke kashe ‘yan jarida ya karu a duniya a karon farko cikin fiye da shekaru goma.
A cikin wani rahoto da aka fitar domin dacewa da Ranar Duniya ta Kawo Karshen Rashin Hukunta Masu Aikata Laifuka kan ‘Yan Jarida hukumar ta bayyana cewa tun daga shekarar 1993 an kashe ‘yan jarida sama da 1,700 a duniya baki daya.
Ta kara da cewa tsakanin shekarar 2024 da 2025 ‘yan jarida da sauran ma’aikatan kafofin watsa labarai 189 sun rasa rayukansu—adadin da ya haura na shekaru biyu da suka gabata da kashi 20 cikin dari.
UNESCO ta ce a cikin kowane shari’o’i 10 a shari’o’i 9 ba a hukunta wadanda suka aikata kisan ba.
Ta kara da cewa duk da cewa kisa shi ne mataki mafi tsanani na takaita aikin ‘yan jarida akwai kuma wasu barazanar da dama da suke fuskanta.
Wadannan sun hada da sace mutane, azabtarwa, da sauran hare-hare na jiki har ma da cin zarafi—musamman a duniyar yanar gizo.
Yankin Gabas ta Tsakiya shi ne yankin da ya fi yawan ‘yan jarida da aka kashe inda aka kashe ‘yan jarida 97 a cikin shekaru biyun da suka gabata da yawa daga cikinsu suna da alaka da yakin da ake yi a Gaza.
Sai dai nahiyar Afirka ma tana ci gaba da fuskantar kalubale masu tsanani.
‘Yan jarida a kasashe irin su Somaliya Uganda da yankin Sahel na fuskantar barazanar kisa tsoratarwa da cin zarafi ta yanar gizo.
A bana kungiyar ‘Reporters Without Borders’ (RSF) ta bayar da rahoton mutuwar ‘yan jarida biyu a nahiyar Afirka: daya a Uganda dayan kuma a Somaliya.
UNESCO ta ce wannan yanayi yana haifar da tsoro ga kwararrun ‘yan jarida wanda hakan ke hana yaduwar bayanai ra’ayoyi da tunani cikin ‘yanci ga dukkan ‘yan kasa.
Haka kuma ta yi gargadin cewa ana kara kai hare-hare kan ‘yan jarida a yankunan da ake fama da rikici ciki har da amfani da jiragen sama marasa matuka (drones).
Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta kuma lura cewa sanya rigar kariya ko kwalkwali mai dauke da alamar ‘yan jarida ba ya bayar da tabbacin tsaro ga ‘yan jarida a wuraren da ake yaki.
Ta yi kira da a kara daukar matakan tabbatar da adalci da kuma kare ‘yan jarida tana mai jaddada cewa alamomin tantance ‘yan jarida ba su ba da garantin kare lafiyarsu ba.
An zabi ranar 2 ga watan Nuwamba ne domin tunawa da kisan ‘yan jarida biyu na gidan rediyon Radio France International a kasar Mali a shekarar 2013
Aisha.Yahaya, Lagos



