{"id":9238,"date":"2026-11-29T10:19:54","date_gmt":"2026-11-29T10:19:54","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=9238"},"modified":"2026-11-29T10:19:54","modified_gmt":"2026-11-29T10:19:54","slug":"jihar-ebonyi-zaben-gwaji-na-inec-ya-gudana-cikin-lumana-tare-da-fitowar-masu-kada-kuria","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/11\/29\/jihar-ebonyi-zaben-gwaji-na-inec-ya-gudana-cikin-lumana-tare-da-fitowar-masu-kada-kuria\/","title":{"rendered":"Jihar Ebonyi: Zaben Gwaji Na INEC Ya Gudana Cikin Lumana Tare Da Fitowar Masu Kada Kuri&#8217;a"},"content":{"rendered":"<p><strong>Atisayen tantance masu jefa \u0199uri&#8217;a da kuma za\u0253en gwaji wanda Hukumar Za\u0253e Mai Zaman Kanta ta \u0198asa (INEC) ta shirya ya gudana cikin kwanciyar hankali tare da fitowar masu son jefa \u0199uri&#8217;a mai gamsarwa a \u0199ananan hukumomin Abakaliki Ezza North da Ezza South na jihar Ebonyi.<\/strong><\/p>\n<p>Ayyukan sun gudana cikin lumana a dukkan \u0199ananan hukumomin uku inda masu son jefa \u0199uri&#8217;a suka fito domin shiga cikin tsarin za\u0253en na gwaji.<\/p>\n<p>A cibiyar gwajin da ke rumfar za\u0253e mai lamba 003 a unguwar Izzi Unuphu Ward 10 masu za\u0253en da suka yi rajista sun riga sun isa wurin domin shiga cikin atisayen.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: INEC Ta Gudanar Da Za\u0253en Gwaji A Rumfunan Za\u0253e 450 A Jihar Kebbi<\/p>\n<p>An gudanar da atisayen a cibiyoyin gwaji da aka ware a fa\u0257in jihar.<\/p>\n<p>Kwamishiniyar Za\u0253e ta INEC a jihar Ebonyi Misis Pauline Onyeka wacce ta sanya ido kan yadda abubuwa ke gudana a rumfar za\u0253e ta Igbudu Eka da ke \u0199aramar hukumar Ezza North ta tabbatar da cewa atisayen ya yi nasara.<\/p>\n<p><em>Onyeka ta ce &#8220;Wannan wani \u0253angare ne na shirye-shiryen INEC domin babban za\u0253en shekarar 2027 kuma an yi shi ne domin gwada ingancin aikin na&#8217;urar tantance masu za\u0253e ta BVAS duba tsarin tantancewar da kuma tantance yadda ake tura sakamakon za\u0253e ta hanyar na&#8217;ura.&#8221;<\/em><\/p>\n<p>Ana gudanar da wannan atisaye na gwaji a fa\u0257in \u0199asar a wasu rumfunan za\u0253e da aka za\u0253a a jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya domin auna shirye-shiryen hukumar ta fuskar fasaha da gudanarwa kafin lokacin za\u0253en.<\/p>\n<p>Ana sa ran INEC za ta yi amfani da bayanan da aka samu daga wannan atisaye domin gano matsalolin fasaha da na tsare-tsare tare da yin gyare-gyaren da suka dace kafin babban za\u0253en 2027.<\/p>\n<p>Jami&#8217;an da ke kula da rumfunan za\u0253en wa\u0257anda suka ha\u0257a da Onu John Egbuhuzor Ahamefula da Godwin Nwokocha sun tabbatar da cewa za\u0253en gwajin ya gudana cikin kwanciyar hankali.<\/p>\n<p>Sai dai \u0257an takarar jam&#8217;iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na majalisar dokokin jihar mai wakiltar Ezza North West Nwafor Joseph ya bayyana cewa an samu \u0199arancin fitowar masu za\u0253e a wasu yankuna na mazabar yayin gudanar da atisayen.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Atisayen tantance masu jefa \u0199uri&#8217;a da kuma za\u0253en gwaji wanda Hukumar Za\u0253e Mai Zaman Kanta ta \u0198asa (INEC) ta shirya ya gudana cikin kwanciyar hankali tare da fitowar masu son jefa \u0199uri&#8217;a mai gamsarwa a \u0199ananan hukumomin Abakaliki Ezza North da Ezza South na jihar Ebonyi. Ayyukan sun gudana cikin lumana a dukkan \u0199ananan hukumomin &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":9241,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[47],"tags":[],"class_list":["post-9238","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-politics"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9238","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9238"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9238\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9242,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9238\/revisions\/9242"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9241"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9238"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9238"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9238"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}