{"id":9058,"date":"2026-11-27T09:08:39","date_gmt":"2026-11-27T09:08:39","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=9058"},"modified":"2026-11-27T09:08:39","modified_gmt":"2026-11-27T09:08:39","slug":"tsoffin-shugabannin-%c6%99asa-sun-jinjina-wa-jagorancin-shugaba-tinubu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/11\/27\/tsoffin-shugabannin-%c6%99asa-sun-jinjina-wa-jagorancin-shugaba-tinubu\/","title":{"rendered":"Tsoffin Shugabannin \u0198asa Sun Jinjina Wa Jagorancin Shugaba Tinubu"},"content":{"rendered":"<p class=\"p1\"><strong><span class=\"s1\">Tsoffin shugabannin mulkin soja na Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya da Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya sun bayyana gamsuwarsu da yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke tafiyar da mulki.<\/span><\/strong><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Janar Ibrahim Babangida ya sake jaddada goyon bayansa ga Shugaban tare da bayyana fatan samun nasararsa a babban zaben shekarar 2027.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Haka nan Janar Abdulsalami Abubakar ya yi kyakkyawan sharhi kan gwamnatin Shugaba Tinubu inda ya bayyana cewa Shugaban ya yi aiki mai kyau tun lokacin da ya hau karagar mulki.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">KARANTA KUMA: Shugaban Kasa Bola Tinubu ya taya tsohon shugaba Babangida murnar cika shekaru 85 \u2013 Voice of Nigeria<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Tsoffin shugabannin biyu sun bayyana wadannan ra&#8217;ayoyi ne a ranar Alhamis yayin da tawagar fadar shugaban kasa karkashin jagorancin Shugaban Ma&#8217;aikatan Fadar Shugaban Kasa Femi Gbajabiamila ta ziyarci gidajensu daban-daban a Minna babban birnin jihar Neja.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Da yake yi wa manema labarai bayani bayan ganawa ta sirri da Babangida Gbajabiamila ya ce tsohon Shugaban mulkin sojan ya yaba da ayyukan gwamnatin Tinubu kuma ya sake jaddada goyon bayansa ga Shugaban.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Shugaban Ma&#8217;aikatan Fadar Shugaban Kasan ya kuma nuna godiya kan ci gaba da goyon bayan da tsoffin shugabannin biyu ke bai wa gwamnatin yana mai jaddada muhimmancinsu a harkokin kasa duba da gudummawar da suka bayar ga tarihin siyasar Najeriya.<\/span><\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"size-full wp-image-9061 alignright\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG_1435.png\" alt=\"\" width=\"414\" height=\"276\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG_1435.png 414w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG_1435-300x200.png 300w\" sizes=\"auto, (max-width: 414px) 100vw, 414px\" \/><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">&#8220;<em>Wadannan mutane ne guda biyu da ba za a iya rubuta tarihin Najeriya ba tare da sun mamaye muhimman sassa a cikin littafin tarihin ba.<\/em><\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">&#8220;<em>Sun kasance masu ba Shugaban kasa goyon baya sosai kuma ya bukaci mu zo mu same su mu gaishe su mu kuma ji yadda suke ciki ina farin cikin ganin cewa dukkaninsu suna cikin koshin lafiya.<\/em><\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\"><em>&#8220;Mun yi tattaunawa mai kyau yanzu haka tare da Janar Babangida wanda yake matukar farin ciki da abubuwan da Shugaban kasa ke yi. Yana gamsuwar kwarai da ayyukansa kuma ya ci gaba da ba shi goyon baya, tare da yi masa fatan alheri da nasara a zaben da ke tafe&#8221;<\/em> in ji Gbajabiamila.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Da aka tambaye shi ra&#8217;ayinsa kan ayyukan Shugaba Tinubu tun lokacin da ya hau mulki Janar Abubakar ya yaba da yadda gwamnatin Tinubu ke tafiyar da al&#8217;amura.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">&#8220;<em>To ya zuwa yanzu abubuwa suna tafiya daidai. Ina ganin Shugaban ya yi aiki mai kyau&#8221;<\/em> in ji shi. Abubakar ya yi kira ga &#8216;yan Najeriya da su tabbatar da zaman lafiya yayin da ayyukan siyasa ke kara karfi kafin babban zaben 2027 yana mai jaddada cewa tashin hankali da rashin zaman lafiya suna kawo cikas ga ci gaban kasa da kuma ingantaccen aikin cibiyoyin dimokuradiyya.<\/span><\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-full wp-image-9063\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG_1434-1.png\" alt=\"\" width=\"414\" height=\"276\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG_1434-1.png 414w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG_1434-1-300x200.png 300w\" sizes=\"auto, (max-width: 414px) 100vw, 414px\" \/><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Da yake magana a madadin Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa (National Peace Committee) Abubakar ya yi kira ga &#8216;yan Najeriya da su ba da fifiko ga shiga harkokin siyasa cikin lumana gabanin babban zaben shekarar 2027. Ya kuma yi gargadin cewa tashin hankali da rashin kwanciyar hankali na iya kawo cikas ga ci gaban kasa tare da raunana cibiyoyin dimokuradiyya.<\/span><\/p>\n<p>&#8220;<em>Ina so in yi addu&#8217;a ga Najeriya domin mu samu zabe cikin kwanciyar hankali saboda a koyaushe ina nanatawa a madadin Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa cewa muna bukatar zaman lafiya a kasar nan.<\/em><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">&#8220;<em>Idan babu zaman lafiya babu kasa kuma idan babu kasa ba za a samu zabe ba. Saboda haka ina rokon al&#8217;ummarmu da su ba wa zaman lafiya dama, domin mu samu zabe cikin lumana&#8221;<\/em> in ji shi.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Haka kuma Abubakar ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa ci gaba da kulla kyakkyawar alaka da tsofannin shugabannin Najeriya duk da nauyin da ke kan sa na tafiyar da mulki da kuma ayyukan yakin neman zabe a fadin kasar.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Tsohon Shugaban Kasan ya kuma nuna godiya ga Shugaban kasar bisa damuwar da ya nuna game da yanayin lafiyarsa da kuma goyon bayan da ya ba shi a lokacin da yake karbar kulawar likita a kasashen waje.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">&#8220;<em>Ina so in gode masa saboda wannan karimci na tunawa da mu duk da cewa lokacin yakin neman zabe ne. Har yanzu yana tunawa da mu cewa muna nan a Minna.<\/em><\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><em><span class=\"s1\">&#8220;Ta hanyarku ina so in gode wa Shugaban kasa bisa goyon bayan da ya saba nuna mana musamman a lokacin da na tafi neman kulawar likita. Ya taimaka min kuma ina gode masa saboda hakan.<\/span><\/em><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">&#8220;<em>Haka kuma a lokacin da Mataimakin Shugaban kasa ya je kasar Indiya domin halartar taron kungiyar BRICS Shugaban ya umurce shi da ya zo ya duba ni ya ga yadda nake&#8221;<\/em> in ji Abubakar.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Tsohon Shugaban Kasan ya kuma yi magana kan ci gaba mai gamsarwa da aka samu a yanayin lafiyarsa inda ya kara da cewa Babangida ma yana cikin koshin lafiya.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\"><em>&#8220;Muna nan lafiya kamar yadda kuka gani. Muna nan kalau kuma lafiyata tana kara inganta sosai.<\/em>&#8221; Ya \u0199ara da cewa \u0257an&#8217;uwana a gefen tudu shi ma yana cikin koshin lafiya.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Tun da farko Gbajabiamila ya bayyana cewa Shugaba Tinubu bayan dawowarsa daga Jihar Borno a ranar Laraba ya umarce shi da ya ziyarci tsoffin shugabannin ya tabbatar da lafiyarsu sannan ya ba shi rahoto yana mai lura da cewa jadawalin ayyukan Shugaban \u0199asa yana da yawa musamman ayyukan kamfen \u0257insa a duk fa\u0257in \u0199asar.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Shugaban Ma&#8217;aikata ya bayyana ziyarar a matsayin gaisuwar girmamawa yana mai bayyana cewa Shugaban ya kuma umarce shi da ya tattauna wasu batutuwa a sirri da tsoffin shugabannin. Ya \u0199ara da cewa tawagar ta riga ta gana da Gwamnan Jihar Neja kafin ta tafi gidajensu.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Daga cikin tawagar akwai Ministan Labarai da Wayar da Kan Al&#8217;umma Alhaji Mohammed Idris Mai Ba Shugaban Kasa Shawara ta Musamman kan Manufofi da Daidaitawa, Hadiza Bala-Usman tsohon Karamin Ministan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci Yusuf Tanko Sununu da kuma tsohon Ministan Sufuri Sa\u2019idu Ahmed Alkali.<\/span><\/p>\n<p class=\"p1\"><span class=\"s1\">Sauran sun hada da Mataimakin Gwamnan Jihar Neja Yakubu Garba dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kuru\/Bebeji Hon. Abdulmumini Jibrin Kofa dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Surulere I Hon. Fuad Kayode Laguda Mai Ba Shugaban Kasa Shawara ta Musamman kan Harkokin Majalisar Dokoki ta Kasa Majalisar Wakilai Dr. Wasiu Olanrewaju-Smart da kuma Darakta-Janar sannan babban mai tattaunawa a Ofishin Najeriya mai kula da Tattaunawar Ciniki (NOTN) Hon. Sanusi Rikiji.<\/span><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Tsoffin shugabannin mulkin soja na Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya da Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya sun bayyana gamsuwarsu da yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke tafiyar da mulki. Janar Ibrahim Babangida ya sake jaddada goyon bayansa ga Shugaban tare da bayyana fatan samun nasararsa a babban zaben shekarar 2027. Haka nan Janar &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":9060,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[39,47],"tags":[],"class_list":["post-9058","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-nigeria-news","category-politics"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9058","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9058"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9058\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9065,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9058\/revisions\/9065"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9060"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9058"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9058"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9058"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}