{"id":8824,"date":"2026-11-24T10:45:23","date_gmt":"2026-11-24T10:45:23","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=8824"},"modified":"2026-11-24T10:45:23","modified_gmt":"2026-11-24T10:45:23","slug":"shugaba-tinubu-ya-sake-jaddada-kudirinsa-na-gudanar-da-mulki-mai-shigar-da-kowa-ciki","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/11\/24\/shugaba-tinubu-ya-sake-jaddada-kudirinsa-na-gudanar-da-mulki-mai-shigar-da-kowa-ciki\/","title":{"rendered":"Shugaba Tinubu Ya Sake Jaddada kudirinsa Na Gudanar Da Mulki Mai Shigar Da Kowa Ciki"},"content":{"rendered":"<p><strong>Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na gudanar da mulki mai shigar da kowa da karfafa hadin kan kasa da tabbatar da adalci ga dukkan &#8216;yan Najeriya. A yayin haka ya nuna godiyarsa ga al&#8217;ummar kabilar Igbo da shugabannin &#8216;yan kasuwa a Legas bisa alkawarin da suka yi na goyon bayan sake zaben sa a ranar 16 ga watan Janairun 2027.<\/strong><\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga matasa dattawa da shugabannin kabilar Igbo a wani taron tattaunawa da kungiyar &#8216;Ndigbo National Dialogue and Development Initiatives&#8217; ta shirya a Cibiyar Al&#8217;adu da Fasaha ta Wole Soyinka (Wole Soyinka Centre for Culture and the Creative Arts) da ke Iganmu a Jihar Legas.<\/p>\n<blockquote class=\"wp-embedded-content\" data-secret=\"HCEwU37akj\"><p><a href=\"https:\/\/von.gov.ng\/president-tinubu-reaffirms-commitment-to-inclusive-governance\/\">President Tinubu Reaffirms Commitment to Inclusive Governance<\/a><\/p><\/blockquote>\n<p><iframe loading=\"lazy\" class=\"wp-embedded-content\" sandbox=\"allow-scripts\" security=\"restricted\" style=\"position: absolute; visibility: hidden;\" title=\"\u201cPresident Tinubu Reaffirms Commitment to Inclusive Governance\u201d \u2014 Voice of Nigeria\" src=\"https:\/\/von.gov.ng\/president-tinubu-reaffirms-commitment-to-inclusive-governance\/embed\/#?secret=qQLY9LjJP7#?secret=HCEwU37akj\" data-secret=\"HCEwU37akj\" width=\"500\" height=\"282\" frameborder=\"0\" marginwidth=\"0\" marginheight=\"0\" scrolling=\"no\"><\/iframe><\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa da mai ba Shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru Mista Bayo Onanuga ya sanya wa hannu Shugaban ya yi kira ga kabilar Igbo da su karfafa hadin kansu su kara shiga harkokin siyasar kasa tare da yin aiki kafada da kafada da sauran kabilu domin gina Najeriya mai zaman lafiya da wadata da hadin kai.<\/p>\n<p><img decoding=\"async\" src=\"https:\/\/von.gov.ng\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/HX1gkJFWsAA6Bp9-1024x683.jpg\" \/><\/p>\n<p>Karanta kuma: Shugaba Tinubu ya dora wa manyan jiga-jigan jam&#8217;iyyar APC alhakin samar da sulhu \u2013 Voice of Nigeria<\/p>\n<p>Shugaban ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fahimci irin gudummawar da al&#8217;ummar Igbo suka bayar wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya inda ya ba su tabbacin cewa babu wani bangare na kasar da za a bari a baya a karkashin tsarin &#8216;Renewed Hope Agenda&#8217;.<\/p>\n<p><img decoding=\"async\" src=\"https:\/\/von.gov.ng\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/HX1gmwTXQAA5J4P-1024x657.jpg\" \/><\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya nuna godiya ga shugabannin kasuwanni daban-daban a Legas wadanda suka ajiye harkokinsu na kasuwanci domin halartar taron.<\/p>\n<p><em>\u201cIna godiya a gare ku duka kan abu guda: kasancewarku a nan a wannan rana. Kun ajiye harkokinku na kasuwanci da neman kudi domin zuwa sauraron shugaban kasa saboda haka dole ne in ce muku na gode\u201d <\/em>in ji shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban kasar ya bayyana kudirinsa na karfafa nasarorin da gwamnatinshi ta samu a fannin tattalin arziki.<img decoding=\"async\" src=\"https:\/\/von.gov.ng\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261123-WA0208-1024x683.jpg\" \/><\/p>\n<p>Ya bayyana cewa ci gaban kasa yana bukatar sadaukarwa daga kowa da fahimtar juna da kuma hadin gwiwa. Ya kuma yi kira ga al\u2019ummar kabilar Igbo da su rungumi tattaunawa da hulda mai amfani domin magance kalubale da kuma ciyar da bukatunsu gaba a cikin tarayyar Najeriya.<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya shaida wa taron cewa dukkan gwamnonin yankin Kudu maso Gabas suna tare da shi a tafiyar da yake yi ta sanya Najeriya ta zama wuri mafi kyau kuma suna aiki domin ganin an sake zaben sa. Ya ambaci sunayen mutane irin su Chief Chidi Anyeagbu mai kamfanin Chisco Motors Dave Umahi Doris Uzoka-Anite da Nkeiruka Onyejeocha wadanda su ma suna wurin taron a matsayin mutanen da ke da kusanci na musamman da shi.<\/p>\n<blockquote class=\"twitter-tweet\" data-width=\"500\" data-dnt=\"true\">\n<p lang=\"en\" dir=\"ltr\">President Tinubu on Monday addressed Ndigbo leaders in Lagos, who promised to support his re-election next January <a href=\"https:\/\/t.co\/f6awjOh8Rw\">pic.twitter.com\/f6awjOh8Rw<\/a><\/p>\n<p>&mdash; Bayo Onanuga, OON, CON (@aonanuga1956) <a href=\"https:\/\/x.com\/aonanuga1956\/status\/2124975346801954860?ref_src=twsrc%5Etfw\">November 23, 2026<\/a><\/p><\/blockquote>\n<p><script async src=\"https:\/\/platform.x.com\/widgets.js\" charset=\"utf-8\"><\/script><\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya bayyana wasu daga cikin dalilan da suka sa ya samar da manufofinsa kamar tabbatar da cewa yajin aikin kungiyoyin ma&#8217;aikata bai sake dakile ayyuka a manyan makarantun gaba da sakandare ba.<\/p>\n<p><em>\u201cDomin kawo karshen rikice-rikicen da ke faruwa a jami&#8217;o&#8217;i da kuma gina kyawawan hanyoyi tare da samar da injiniyoyin da za su kula da motocinmu dole ne yaranmu su kasance a makaranta. Kasancewarsu daga gidan talauci ba ya nufin cewa bai kamata su shiga jami&#8217;a ko su samu ci gaba ba.<\/em><\/p>\n<p><img decoding=\"async\" src=\"https:\/\/von.gov.ng\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261123-WA02131-1024x690.jpg\" \/><\/p>\n<p><em>\u201cMuna aiwatar da hakan ta hanyar shirin NELFUND. A yau jami&#8217;o&#8217;i sun samu kwanciyar hankali saboda muna yin abin da ya dace. Muna zuba jari a fannonin noma da kasuwanci duk wanda ke harkar kasuwanci zai iya neman lamuni daga Bankin Masana&#8217;antu (Bank of Industry) yayin da masu aikin noma za su iya samun lamuni na kananan manoma.<\/em><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><em>\u201cDole ne mu kula da wannan kasa saboda amfanin kowannenmu. Wani muhimmin sashi na taken kasar nan shi ne abin da ya sa nake tsaye a nan. Na nemi damar yin hakan kuma a shirye nake na yi wa kasa hidima.\u201dhttps:\/\/von.gov.ng\/president-tinubu-reaffirms-commitment-to-inclusive-governance\/<\/em><\/p>\n<p>https:\/\/pbs.twimg.com\/media\/HX1nJOkWkAArN30?format=jpg&#038;name=240&#215;240<\/p>\n<p>A nata bangaren tsohuwar Ministar Jiha ta Ma\u2019aikatar Kwadago da Samar da Ayyuka Hon. Nkeiruka Onyejeocha ta bai wa Shugaba Bola Tinubu tabbacin goyon bayan kabilar Igbo ga yunkurinsa na sake tsayawa takara a shekarar 2027. Ta bayyana cewa taruwar shugabanni da masu ruwa da tsaki na kabilar Igbo a Legas shaida ce ta dunkulewarsu waje guda da kuma nuna amincewarsu ga Shugaban.<\/p>\n<p>Ta ce al\u2019ummar sun fahimci muhimmancin kulla kawancen siyasa da sauran yankunan kasar domin cimma burinsu na ganin an zabi dan kabilar Igbo a matsayin Shugaban kasa a nan gaba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>LAAN NASIDI.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na gudanar da mulki mai shigar da kowa da karfafa hadin kan kasa da tabbatar da adalci ga dukkan &#8216;yan Najeriya. A yayin haka ya nuna godiyarsa ga al&#8217;ummar kabilar Igbo da shugabannin &#8216;yan kasuwa a Legas bisa alkawarin da suka yi na goyon bayan sake &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":8827,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[47],"tags":[],"class_list":["post-8824","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-politics"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8824","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8824"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8824\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8828,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8824\/revisions\/8828"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8827"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8824"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8824"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8824"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}