{"id":8789,"date":"2026-11-23T07:51:34","date_gmt":"2026-11-23T07:51:34","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=8789"},"modified":"2026-11-23T07:51:34","modified_gmt":"2026-11-23T07:51:34","slug":"shugaba-tinubu-ya-dora-wa-mangan-jamiyyar-apc-alhakin-samar-da-sulhu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/11\/23\/shugaba-tinubu-ya-dora-wa-mangan-jamiyyar-apc-alhakin-samar-da-sulhu\/","title":{"rendered":"Shugaba Tinubu Ya Dora Wa Mangan Jam&#8217;iyyar APC Alhakin Samar Da Sulhu"},"content":{"rendered":"<p><strong>Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci shugabannin jam&#8217;iyyar All Progressives Congress (APC) da su \u0199ara himma wajen sulhuntawa ha\u0253aka yafiya da \u0199arfafa \u0199ungiyoyin jama&#8217;a don \u0199ara yawan masu jefa \u0199uri&#8217;a da kuma tabbatar da nasarar jam&#8217;iyyar a babban za\u0253en 2027.<\/strong><\/p>\n<p>Shugaban ya yi wannan kiran ne a wani taron addu&#8217;o&#8217;i na musamman da iyalan Tinubu suka shirya don goyon bayan sake tsayawa takararsa a karo na biyu wanda aka gudanar a Yoruba Tennis Club Onikan Lagos.<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya yi kira ga shugabannin jam&#8217;iyyar da su ajiye koke-koken kansu su warware bambance-bambancen cikin gida sannan su tuntu\u0253i membobin da suka fusata a fa\u0257in \u0199asar yana mai jaddada cewa <em><strong>ha\u0257in kai da sulhu suna da matu\u0199ar muhimmanci ga nasarar za\u0253en jam&#8217;iyyar.&#8221;<\/strong><\/em><\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-8793\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261122-WA0074-768x512-1-300x200.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"200\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261122-WA0074-768x512-1-300x200.jpg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261122-WA0074-768x512-1.jpg 768w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Ya ba da umarni musamman ga Mashawarcinsa na Musamman kan Harkokin Siyasa Alhaji Ibrahim Kabiru Masari da tsohon Ministan Tsaro Alhaji Abubakar Badaru da su koma yankunansu na siyasa domin sasanta su da masu ruwa da tsaki da ke da korafi tare da fadada kokarin samar da zaman lafiya zuwa Jihar Jigawa da sauran sassan kasar.<\/p>\n<p><em><strong>\u201cAlhaji Kabiru Masari ka koma gida ka sasanta kowa da kowa. Wannan shi ne umarnin Shugaban Kasa. Idan ka kammala hakan sai ka wuce zuwa Jigawa. Ka je sauran wurare ma ka sasanta mutane ka roke su domin dole ne mu sasanta kuma duk wani fushi ya kamata ya gushe gaba daya,<\/strong><\/em>\u201d in ji Shugaban Kasa.<\/p>\n<p>Shugaban na Najeriya ya tuno da irin gogewarsa ta shawo kan sabani a siyasa a tsakanin shekarun 2021 da 2022 inda ya bayar da misali da dangantakarsa da marigayi tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a matsayin shaida kan muhimmancin gafara da kuma nuna sassauci a siyasa.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: 2027: Shugaba Tinubu na Neman Nasarar APC Ya Yi Alkawarin Kawo Ci Gaba Sabani a Siyasa<\/p>\n<p><strong>Sabanin Ra&#8217;ayi Na Siyasa<\/strong><\/p>\n<p>Ya jaddada cewa sabani a siyasa bai kamata ya zama cikas ga cimma manufofin da aka sanya a gaba ba inda ya yi kira ga magoya bayan jam\u2019iyyar da su maye gurbin fushi da sulhu tare da sabunta jajircewarsu wajen cimma burin jam\u2019iyyar a zabe.<\/p>\n<p>Dangane da batun fitowar masu zabe Shugaba Tinubu ya nuna damuwarsa kan karancin yawan mutanen da suka fito zabe a Jihar Lagos yana mai tambayar dalilin da ya sa a cikin masu zabe da suka kai kimanin miliyan bakwai da suka yi rajista kuri\u2019u tsakanin 100,000 zuwa 200,000 kawai aka samu.<\/p>\n<p><em><strong>\u201cKo da kun yi nasara kuma kuka ce nasara dai nasara ce\u2014a\u2019a ba haka ba ne. Dole ne ku samar da iyakar adadin da za a iya samu. Kuma ga dukkaninku ina so ku sani cewa fushi ba zai magance komai ba,\u201d<\/strong> <\/em>in ji Shugaba Tinubu.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-8794\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261122-WA0077-750x420-1-300x168.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"168\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261122-WA0077-750x420-1-300x168.jpg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261122-WA0077-750x420-1-390x220.jpg 390w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261122-WA0077-750x420-1.jpg 750w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Ya yi kira ga magoya bayansa da su karfafa gwiwar \u2018yan Najeriya da suka cancanta wajen karbar katunan zabe na dindindin (PVC) da kuma shiga harkokin zabe mai zuwa sosai inda ya jaddada cewa<em><strong> \u201cnasara a zabe ya kamata ta samu goyon bayan fitowar jama\u2019a da yawa don kada kuri\u2019a.\u201d<\/strong><\/em><\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya ce:<br \/>\n<strong>\u201cShugaban ya tuna cewa ya yi amfani da manufar \u2018Emilokan\u2019 (lokacina ne) a shekarar 2022. Yanzu kuma lokacinku ne (\u2018Eyinlokan\u2019) don ganin an sake zabe na.\u201d<\/strong><\/p>\n<p>Ya yi kira ga al\u2019ummar jihar Legas da su fito da yawa a ranar zabe Mai zuwa domin gudanar da hakkinsu na kada kuri\u2019a.<\/p>\n<p>Yayin da yake tunawa da kalubalen da suka gabaci zaben shugaban kasa na 2023 Shugaban ya ambaci wahalhalun tattalin arziki da karancin kudi da \u2018yan Najeriya suka fuskanta inda ya danganta nasarar da ya samu a zaben ga taimakon Allah da kuma jajircewar magoya bayansa.<\/p>\n<p><em><strong>\u201cMun nemi taimakon Allah Madaukakin Sarki wanda idan Ya ce \u2018Kun faya kun\u2019 (Kasance sai ya kasance). Hakan ya kai mu ga nasara kuma yanzu muna rike da shugabancin kasa. Allah yana ba da iko ga wanda Ya so kuma yana kwace shi daga wanda Ya so,\u201d<\/strong> <\/em>in ji Shugaban.<\/p>\n<p>Ya amince cewa kalubalen siyasa da ke gabansu ba su da wuyar gaske idan aka kwatanta da wadanda aka fuskanta a 2023 amma ya gargadi \u2018yan jam\u2019iyyar da su guji sakaci ko rashin daukar abubuwa da muhimmanci.<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya kuma jaddada muhimmancin imani godiya da gafara inda ya bayyana darussan da ya koya daga ziyarar da ya kai kwanan nan a dakin Allah (Ka\u2019aba) tare da kira ga magoya bayansa da su nuna wa wasu gafara kamar yadda suke nema daga Allah Madaukakin Sarki.<\/p>\n<p><em><strong>\u201cA shekarar 2021-22 ni ma na taba jin haushi. Zan iya tunawa da lokacin Muhammadu Buhari; lokacin da ya kira ni na amince. Ya ce ni ne mai gudanarwa kuma shugaban hadin gwiwa na yakin neman zabe sai na ce to shikenan. Duk da cewa na ji haushi da radadi a lokacin na yafe,\u201d<\/strong> <\/em>in ji shi.<\/p>\n<p>Shugaban ya nuna godiya ga iyalan Tinubu saboda addu\u2019o\u2019insu da goyon bayansu na tsawon lokaci a duk tsawon tafiyarsa ta siyasa yayin da ya kalubalanci matasan Najeriya da su rungumi nauyin jagoranci tare da bayar da gudummawa mai ma\u2019ana wajen ci gaban kasa.<\/p>\n<p>Ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na magance matsalolin ababen more rayuwa da kalubalen ci gaba inda ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa Najeriya tana da karfin shawo kan duk wani cikas ta hanyar hadin gwiwa da kuma ci gaba da kokari.<\/p>\n<p><em><strong>\u201cZa mu iya cimma hakan a wannan \u0199asa. Babu abin da ba za mu iya yi ba. Ko ka\u0257an. Duba Abuja mun kawar da manyan duwatsu. A Legas mun shawo kan Tekun Atlantika. A Abuja mun kawar da duwatsu domin ba da damar ci gaba. Babu abin da ba za mu iya yi ba idan muka sa ranmu a kai,\u201d<\/strong><\/em> in ji Shugaba Tinubu<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-8795\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261122-WA0076-768x512-1-300x200.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"200\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261122-WA0076-768x512-1-300x200.jpg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261122-WA0076-768x512-1.jpg 768w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Ya sake jaddada kudirinsa na samar da shugabanci mai ma&#8217;ana karfafa hadin kan kasa da adalci tare da gina kasa mai wadata ga dukkan &#8216;yan Najeriya.<\/p>\n<p>Gwamnan Jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu ya bayyana Shugaban Kasa a matsayin misali na adalci daidaito da kuma shugabanci mai shigar da kowa inda ya siffanta wadannan halaye a matsayin ginshikai masu muhimmanci wajen gina Najeriya mai hadin kai da zaman lafiya da wadata.<\/p>\n<p>Shugaban taron kuma dattijo mai girmamawa Alhaji Lateef Femi Okunnu mai shekaru 94 a duniya ya yi alkawarin yin kamfen da kuma kada kuri&#8217;a ga Shugaban Kasa a ranar 16 ga watan Janairun 2027.<\/p>\n<p>Ya ce <em><strong>&#8220;Shugaban Kasa ya yi abubuwa da dama da suka cancanci a sake zabensa.&#8221;<\/strong><\/em><\/p>\n<p>Dattijon ya kuma jaddada muhimmancin tabbatar da adalci yana mai cewa <em><strong>&#8220;Gwamnatin Tinubu tana mayar da hankali kan tattalin arziki da ababen more rayuwa musamman babbar hanyar da ke bi ta bakin teku daga Lagos zuwa Calabar da kuma babbar hanyar da ta tashi daga Sokoto zuwa Badagry tare da karfafa darajar Naira da kuma adadin kudaden waje da kasar ke ajiyewa.&#8221;<\/strong><\/em><\/p>\n<p>A yayin gabatar da jawabin godiya wakilan iyalan Tinubu Alhaji Rafiu Tinubu da Alhaja Iyalode Bintu Tinubu sun gode wa Allah bisa ni&#8217;imomin da ya bai wa iyalan sannan suka yi kira ga &#8216;yan Najeriya da su goyi bayan Shugaban Kasa a kudirinsa na tabbatar da cewa jama&#8217;a sun ci moriyar dimokuradiyya.<\/p>\n<p>Mai gudanar da zaman addu&#8217;ar wanda kuma shi ne Babban Limamin Jihar Lagos Sheikh Sulaimon Oluwatoyin Abou-Nolla ya karanta ayoyi daga littafin Alkur&#8217;ani mai girma tare da rokon Allah ya ba wa Shugaban Kasa nasara a dukkan al&#8217;amuransa da kuma lafiya mai dorewa.<\/p>\n<p>Zaman addu&#8217;ar ya samu halartar Gwamnan Jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq Gwamnan Jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu Mataimakinsa Kadiri Obafemi Hamzat Mai ba Shugaban Kasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu Shugaban Ma&#8217;aikatan Fadar Shugaban Kasa Femi Gbajabiamila da kuma Ministan IIimi Dr. Tunji Alausa.<\/p>\n<p>Sauran manyan baki da suka halarci taron sun hada da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Lagos Mudashiru Obasa Babban Limamin Jihar Lagos Sheikh Sulaimon Oluwatoyin Abou-Nolla; da kuma Shugaban Kwamitin Amintattu na kungiyar <em><strong>&#8216;Coalition of Northern Groups&#8217;<\/strong><\/em> Dr. Nasturah Ashir Sharriff. Alhaji Lateef Femi Okunnu &#8216;yan uwa da abokanan jam&#8217;iyyar Tinubu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Aisha.Yahaya, Lagos<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci shugabannin jam&#8217;iyyar All Progressives Congress (APC) da su \u0199ara himma wajen sulhuntawa ha\u0253aka yafiya da \u0199arfafa \u0199ungiyoyin jama&#8217;a don \u0199ara yawan masu jefa \u0199uri&#8217;a da kuma tabbatar da nasarar jam&#8217;iyyar a babban za\u0253en 2027. Shugaban ya yi wannan kiran ne a wani taron addu&#8217;o&#8217;i na musamman da iyalan Tinubu &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":8792,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[47],"tags":[],"class_list":["post-8789","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-politics"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8789","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8789"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8789\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8796,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8789\/revisions\/8796"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8792"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8789"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8789"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8789"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}