{"id":8756,"date":"2026-11-22T12:47:15","date_gmt":"2026-11-22T12:47:15","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=8756"},"modified":"2026-11-22T12:47:15","modified_gmt":"2026-11-22T12:47:15","slug":"shugaba-tinubu-ya-yaba-da-gudummawar-da-betara-ya-bayar-a-majalisa-a-shekaru-60","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/11\/22\/shugaba-tinubu-ya-yaba-da-gudummawar-da-betara-ya-bayar-a-majalisa-a-shekaru-60\/","title":{"rendered":"Shugaba Tinubu Ya Yaba Da Gudummawar Da Betara Ya Bayar A Majalisa A shekaru 60"},"content":{"rendered":"<p><strong>Shugaba Bola Tinubu ya yaba wa dan majalisar da ke wakiltar mazabar tarayya ta Biu\/Bayo\/Shani\/Kwaya Kusar a jihar Borno Muktar Aliyu Betara saboda gudunmawar da ya bayar wajen tsara dokoki a Majalisar Dokokin Tarayya. Musamman ma ya jinjina masa kan jajircewarsa wajen samar da dokokin da ke da nufin inganta walwalar &#8216;yan kasa karfafa tattalin arziki da kuma inganta tsaron kasa.<\/strong><\/p>\n<p>Shugaban ya bayyana wannan yabo ne a cikin sakon taya murna dangane da cika shekaru 60 da haihuwar dan majalisar a ranar Lahadi 22 ga watan Nuwamba inda ya amince da irin rawar da ya taka wajen ayyukan majalisa da kuma dadewa yana hidima a Majalisar Wakilai.<\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru Bayo Onanuga ya fitar Shugaba Tinubu ya bayyana nasarorin zabe da Betara ya samu a jere a matsayin shaida kan ingancin wakilcinsa da kuma amincewar da mutanen mazabarsa suka nuna gare shi.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Betara Ya Samu Tikitin Takarar APC Ba Tare da Hamayya Ba A Mazabar Biu<\/p>\n<p>Shugaban ya kuma yaba wa dan majalisar saboda sanya walwalar al&#8217;umma a gaba da kuma samar da tallafi ga mazauna yankin da ke cikin bukata yana mai nuni da cewa jajircewarsa ga mutanen mazabarsa ce ta sa aka ci gaba da zabensa a kai a kai.<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya shiga cikin iyalan Betara abokansa da abokan aikinsa wajen murnar cika shekaru 60 da haihuwarsa inda ya yi masa fatan samun koshin lafiya karin karfi da kuma karin shekaru masu yawa na ci gaba da hidima ga mutanen mazabarsa da kasa baki daya.<\/p>\n<p>Betara wanda kwararren akawu ne an zabe shi a karon farko a Majalisar Wakilai a shekarar 2007 kuma tun daga lokacin ya sake samun nasarar zabe sau hudu a jere inda ya yi aiki a Majalisun Dokokin Tarayya na shida bakwai takwas tara da kuma na goma.<\/p>\n<p>A baya ya taba zama shugaban kwamitin majalisa kan kasafin kudi (Appropriations) a lokacin Majalisa ta Tara kuma a halin yanzu shi ne shugaban kwamitin majalisa mai kula da Babban Birnin Tarayya (FCT).<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaba Bola Tinubu ya yaba wa dan majalisar da ke wakiltar mazabar tarayya ta Biu\/Bayo\/Shani\/Kwaya Kusar a jihar Borno Muktar Aliyu Betara saboda gudunmawar da ya bayar wajen tsara dokoki a Majalisar Dokokin Tarayya. Musamman ma ya jinjina masa kan jajircewarsa wajen samar da dokokin da ke da nufin inganta walwalar &#8216;yan kasa karfafa tattalin &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":8759,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[39,48],"tags":[],"class_list":["post-8756","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-nigeria-news","category-entertainment"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8756","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8756"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8756\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8760,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8756\/revisions\/8760"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8759"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8756"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8756"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8756"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}